Tuesday, 13 September 2016

BABBAR SALLAH A JIHAR KATSINA

Anyi Sallah Za'a Bar Baya-da-Kura:

Duk lokacin da aka ce sallah tazo, tun ranar jajibiri wato ranar Arfat, gari yake canjawa daga warin kwatoci, ko warin rubewar bololi, da kuma warin rumar ajiyar tsofaffin kayan. Gari hakan cika da kamshin soye-soyen naman Kaji don sune akafi yankawa a wannan rana ta Arfat, kowa zaka Ganshi cikin annashuwa da kazar-kazar na kokarin shirya kanshi don jiran washegarin ranar Sallah.

A wannan karon, jama'a na cikin halin babu da kuma rashin sanin madafar dafawa don taimakawa jukkuna da abinda zasu ci su samu kwarin guiwar aikata katabus a ranar Sallah. Duk da haka, da yawa daga mutane basu karaya ba, abinda suke dashi shine dai abinda zasuyi amfani dashi. Wannan yasa tun a shekaran jiya Jajibiri rawa ta canja tunda dai Kid in shima ya canja, masu halin Kaji na soyawa, masu halin siyen nama na siye suna soyawa. Haka dai kowa ya kasance cikin shirin zuwan Babbar Rana.

A jiya Litinin, Ranar Sallah, ranar Layya, ko ina ka duba zaka Tara's da Mutane manya da yarda, maza da mata kowa yaci ado da kwalliya don nuna murnar wannan babbar rana ta layya. Duk da kasancewar garuruwa da dama anyi Ruwa, hakan bai kawo cikas wajen fitowar jama'a zuwa masallatan da ake gabatar da wannan babbar Sallah ba. Cikin Ikon Allah, anyi Sallah lafiya an kuma yi Yankan Layya lafiya. Har zuwa dare, wurare kadan ne zakaji inda aka samu Matsaloli a wannan rana.

Yau ma dai Jihar tamu ta Katsina cike take da mutane don kallon Hawan Bariki. Alhamdulillah bawa ya gunada cikin nasara da kuma tsaro. Sannan mutane a cikin gida sun gyara ragunansu da kuma sauran nau:'o'in dabbobin da suka yanka a matsayin Layya. Yara kanana kuwa tuni suka fara cin ado suna lekawa gidajen 'yan uwa da abokanan arziki don yi masu barka da Sallah a matsayin "Yawon Sallah".

A nan Nike so nayi amfani da wannan damar wajen Kiran iyayenmu, dasu kula matuka akan 'ya'yansu mata. A wannan irin ranakun ne iyaye ke da dabi'ar barin 'yayansu mata suyi abinci don kaiwa Samarinsu. Tabbas wannan babban kuskurene, don a irin wannan lokaci komai zai iya faruwa walau da yardar matan ko da rashin yardarsu. Allah ya kiyaye.

Daga karshe ina Rokon Allah ya maimaita mana, ya karbi ibadun da mukayi, Allah ya kara tsawon kwanaki har mugs zuwan wata sallar idan kuma mun mutu Allah ya jikanmu da rahamarshi Amin.

Ku ajiye Ra'ayoyinku a Comment Box don jin yadda kuka gudanar da sallarku ta Layya...

No comments:

Post a Comment