Tuesday, 20 September 2016

YARAN ZAKZAKY SUNYI ALLAH WADAI DA GWAMNATIN BUHARI


Gwamnatin Nigeria a ranar Juma'ar data gabata ta bayar da dalilan da yasa. Take ci gaba da tsare Ibrahim El-Zazzaky, shugaban kungiyar Shi'a ta kasa.

Sai dai hakan ya jawo bacin ran wasu mabiya shi'ar inda har suka kara zage damtse wajen kudirinsu na komawa Abuja da zama har sai an fito da shugaban nasu. A kowane lokaci, abinda sukafi cewa shine mutanensu 300 da sojoji sukayiwa kisan gilla, sannan sunyi Allah wadai da wannan gwamnati ta El-Rufai dama shugaban Kasa Buhari.

Kamar yadda ya fada a yayin gabatar da jawabi, Ministan harkokin wajen kasar Nigeria, Geoffrey Onyeama, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bata da niyyar tsoma baki akan tuhumar da gwamnatin Jihar Kaduna takeyiwa shugaban na Shi'a.

Idan ba'a manta ba, Gwamnatin Jihar Kaduna a loton baya kadan ta saki rahoto dangane da wani kwamiti data hada don binciken karon battar da akayi tsakanin Sojojin Nigeria da kuma mabiya akidar Shi'a wanda Har yai sanadin kisan gillar mutane 300 daga cikin mabiya shi'ar.

Wasu 'yan Shi'a da sukayi bayani sunce "Akalla jama'arsu 100 ne tare da shugaban nasu Ibrahim El-Zazzaky da Matarshi ne suke tsare a hannun hukuma ba tare da ana barinsu ganawa da su ba"

Tsawon lokacin da Zazzaky ya dauka a kulle, an hanashi ganawa koda da Likita ko Lauyanshi, hada iyalan gidabshi. A ranar 5 ga watan April, lauyoyin Musulunci sun sami damar ganawa da shi, inda suka tabbatar da makancewar ido daya na Zakzaky.

"Sakamakon mummunan farmakin da aka kai masu, Sheikh Zakzaky ya rasa idonsa na hagu inda likitoci ke kokarin ceto dayan idon don kada ayi biyu-babu ko-daya," Lauya Femi Falana ya fadi hakan.

Mabiya akidar ta Shi'a dai tuni suka shirya tsaf wajen yin addu'a da kuma kokarin yin zanga-zangar Lumana a Babban Birnin Tarayya Abuja a kokarinsu na ganin an sako Shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

DONT FORGET TO SHARE...


No comments:

Post a Comment