Monday, 1 August 2016

SHARI'AR MUSULINCI KO SIYASA? Daga Mansur Halilu

Yanzu ne yafi cancanta Malaman addini su fito su nemi a tabbatar da SHARI'AR MUSULINCI a arewa ko arewacin Najeriya, duba da irin dasawar dake tsakanin malamai da Gwamnatin APC mai mulki tun daga matakin jaha har tarayya Idan muka lura da kyau zamu fahimci Malamai sunyi sanyi game da wannan niyya, gwuiyawun su kuma sunyi rauni don haka nake kira tare da zaburar dasu su farka su cigaba da gwagwarmayar kamar yadda akayi a wasu shekarun baya (1999-2003) .

Abin yayi matukar tasiri a wancan lokaci duk da bai samu amincewa ba daga gwamnatin jiha ta wancan lokaci Wannan yasa nake ganin idan har da gaske ake to yanzu ne lokaci mafi dacewa da irin wannan gwagwarmaya duba da irin halin da al'umma ta tsinci kanta a yau!


Sakamakon kaucema SHARI'AR ALLAH da akayi, da kuma dogaro da wasu zantukan ashararai yayin yin hukunci, ko shakka babu wannan na daya daga cikin abubuwan da suka kaimu inda muke a yau (HALIN TABARGAZA, HARMAGAZA DA HARIGIDO).

Daga karshe ina kira ga Dukkan wani malami, masu rike da madafan iko, masu fada aji da talakawa yan'uwana duk wanda zai iya yin wani abu game da wannan to mugani a kasa. Indai da gaske addini ake mawa ba aljihunanmu ba to zamu gani.

Ina rokon Allah ya kara haska mana hanya madaidaiciya ya kuma bamu ikon bin ta. Amin

No comments:

Post a Comment