Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari ya iso makarantar Firamare dake kauyen kudu na cikin karamar hukumar Matazu domin kaddamar da shirin bada tallafin karatu (Scholarship) ga dalibai mata 'yan aji daya da kuma 'yan ajin share fagen shiga aji dayan.
Wannan shiri, daya ne daga cikin shirin hada ka domin tallafawa wa ilmi musamman na 'ya'ya mata, kuma ana gudanar dashi ne tare da gudummuwar Bankin Duniya da kuma wata kungiya mai zaman kanta mai suna 'Global Partnership for Education'.
An fito da wannan shiri ne domin sauwake wa iyaye hidimar karatun yaran tare kuma da barin 'ya'yan su mata su rika zuwa makaranta maimakon dora masu Talla.
No comments:
Post a Comment