Saturday, 6 August 2016

Sako Daga Matasan Dutsinma Zuwa Ga Sanata Umar Ibrahim Kurfi [Nzeribe]

Senator Kurfi

Sako Daga Matasan Masu Zamankansu Na Karamar Hukumar Dutsin-Ma Jihar Katsina (Independent Youth Forum In a Collaboration with All Progress Congress Dutsin-Ma Local Government Katsina State Chapter) Zuwa ga Senator Umar Ibrahim Kurfi Enzarebe. 

Yau kimanin Shekara Daya kenan da wata uku da hawanka akan karagar mulkinka amman babu wanda zaice ga project ko wani empowerment dakayi ma jama'ar karamar hukumar Dutsin-Ma. Babu wanda ka nada wanda jama'a zasu kaima kokensu abun ya iso gareka.

Mutuwa, Biki, Taro, ziyara ko makamancin haka babu wanda ka tabayi a garin Dutsinma, a lokacin baya dakayi rep na kurfi/Dutsinma miyasa duk baka nuna mana wannan Halayyar takaba? Har aka gama campaign naka babu wata kungiya ko tarin mutanan da kaba kudi ballantana kace dan kudin ka aka zabe ka, idan ka cire Shugaba Buhari Duk Dutsin-Ma babu wanda ya samu yawan kuru'un ka. 


Ka raina jama'ar Dutsin-Ma baka daukar waya haka zalika baka maido reply message idan an yi maka ko dae maganar da kafadima yan Dutsinma lokacin campaign dinka hakane baka chanza ba???
Muna sane da duk wani motsinka da kuma adadin kaya da kudi da sauransu wanda ake baku ku ba jama'ar dakuke wakilta Amman kowa yayi dakyau zaiga da kyau....


Follow Our twitter handle: @Cliqq_Magazine

Like Our Facebook Page: Cliqq Magazine
Email: cliqqmagazine.@gmail.com
Blog Address: Cliqqmagazine.blogspot.com

Tel No: 08062883759
Please share your thoughts in the comment box below
 


1 comment:

  1. 1. Zai zauna a Abuja yayi aikin da aka tura shi yayi ne ko zai dawo Dutsinma ya rika zuwa biki da suna yana baku kudi?
    2. Ina zai samo kudin da zai rika raba maku?
    3. Dutsinma kadai ce a Katsina Central?
    4. Aikin dan majalissar dattawa ne ya zo yayi maku project?

    ReplyDelete