Ba batun balullubar lissafi da kididdiga zan yi ba,ba ma zan bata lokacina ba
kan hakan,sai dai ganin yadda a kasar nan duka ake cikin halin kasa juya waina
daga mai tanda,kuma shirye-shiryen bunkasa rayuwar al'umma bai fi na habaka
kasuwanci da sana'o'i ba musamman ma ga matasa.
Amma a jihata ta Katsina sai kawai aka ware kudade har Miliyan 104 aka rabawa mata awakai da bunsura don su kiwata.
Abu ne da ana iya lullube shi da kyautatawa,amma kuma za a iya yi masa tumbur da cewa ba shi ne abin da 'yan jihar ke bukata ba.Kuma ba zai zamo mafi muhimmanci ba idan aka sanya shi a bisa faifan kaso bayan nema da lalubo shawara.
Ya dai kamata a rika rike madogara babba kafin a sawo awakan da mafi yawanci akwai a cikin gidajen kananan Hukumomin jihar 34.
#Bahaushe.
05.08.2016.
Follow Our twitter handle: @Cliqq_Magazine
Like Our Facebook Page: Cliqq Magazine
Email: cliqqmagazine.@gmail.com
Blog Address: Cliqqmagazine.blogspot.com
Tel No: 08062883759
Please share your thoughts in the comment
box below
No comments:
Post a Comment