Monday, 8 August 2016

Karanta Labarin Inda Aka Kara Tsintar Jariri Cikin Tayar Mota A Katsina


An kara tsintar jariri kunshe a cikin tayar Mota a bayan Mangal Plaza wanda ke kallon Magama Food Restaurant a Katsina.

A kwankin baya cikin watan Azumi da ya gudana, Cliqqmagazinehausa.blogspot.com ta buga rahotun jariri da aka tsinta a cikin bola dake unguwar Daki Tara.
Cliqqmagazinehausa.blogspot.com  Ta samu wannan labari ne daga shafin yanar gizo gizo na Facebook da “Amina Sa’ad Ruma ta rubuta kamar haka” “Innalillahi Wainna Ilaihirrajun
Wannan Masifa Dami Tayi Kama, wannan wani jinjiri ne daka tsinta acikin taya da safiyar yau, abayan mangal plaza oppsite magama restaurant.


Ina kira ga yan uwana mata da muji tsoron Allah musani wannan sabon Allah ne mafi muni, kuma Allah yayi tanadin azaba mai radadi ga masu aikata wannan aika aika. Allah ya tsare mana imaninmu.”

Wanna ba karamin masifa bane ke faruwa a nan cikin jihar Katsina, wanda ya jaza masifu daban daban wa al’umma. 

Shin ko taya ya za’a iya magance wannan matsala?

No comments:

Post a Comment