Cigaba da aiki a kanfanin zai kawo cigaba musamman wajen inganta tattalin arzikin Jihar Katsina ta hanyan samar da aiki ga jama’ar Katsina.
An sami wannan nasara ta hadin guiwa da wani kamfanin kasar India mai sunan M/S AMPRI GLOBAL LIMITED wanda suka sami shigowa Jihar nan ta taron habaka tattalin arzikin Jihar (Economic and Investment Summit) da ya gudana cikin watan Mayu da ya gabata.
Baya ga kusa, nan gaba, wannan kamfani za a fadada shi ya kai ga yana hada Kekunan hawa, Babura da kuma Keke NAPEP.
Wannan Kamfani dai Gwamnatin tsohuwar Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Alhaji AbdulKadir Balarabe Musa ta assasa shi domin habaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi, amma sai a wannan lokacin Allah Yasa aiki zai kankama a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari CFR, Dallatun Katsina.
No comments:
Post a Comment