1. "masu mulki ire-iren wadanda zalunci ne ke
cike da zukatansu za su samu hanyar azurta kansu cikin sauqi sakamakon ga man
nan ya samu a yankinsu ba sai sun sha wata wahalar ta da jijiyar wuya a
majalisun da suke haduwa da 'yan kudu ba"
2. "kusan dukkanin hankalin 'yan Arewa zai
koma kan shi
man na fetur inda kusan ko'ina matasa za su dauki makamai su shiga yin ayyukan
ta'addanci domin fatan gwamnati ta kira su ta yi sulhu da su da nufin ba su
haquri kamar yadda aka yi yanzu a yankunan Niger/Delta"
3. "sannan kuma dukkanin yankunan da ake yin
ayyukan noma za a daina yi... domin ganin ga man fetur ya samu kawai kowa zai
sa ran zai ci banza"
4. "haka nan kuma mafi 85% na ma'aikatan da za
su amfana wajen ayyukan tonon man ba 'yan Arewar ba ne... domin kusan gogaggun
Engineers (injiniyoyi) ake nema koda kuwa daga ina za su zo ba ruwan man fetur
da wanda bai yi karatun tononsa har zuwa matakin "MASTERS" a 'kalla
kenan"
5. har wala yau man fetur na da adadin shekarun da
zai 'kare a rasa shi a sa'ilin da kuma an rigaya an gama lalatar da filaye da
gonakin noman da jikokinmu masu zuwa nan da shekaru-100 za su so a ce sun
gudanar da ayyukan nomansu a kai. ...................
Amfanin aikin noma ga mutanen Arewa 99%
"amfanonin kuwa ba za su taba 'kirguwa ba" ..................amma ga
wasu daga ciki...............
1. Samar da
abinci.
2. Raya 'kasar noma.
3. Samar da aiki
musamman ma ga wadanda ALLAH bai huwace musu damar yin karatun boko mai zurfi
ba!
4. Ciyar da wasu al'ummomin da ba su yin noma.
5. Taimakawa 'kananan 'kwari samun abinci.
6. Yin riga-kafin ambaliyar ruwan sama!
7. Hana kwararowar hamada.
8. Samar da Arziki
mai yawa mai albarka.
9. Gadar wa 'yan baya abin yi mai amfani.
10. Nuna wa ALLAH godiya da kyautar ruwan sama.
...................
Cutarwar aikin noma ga mutanen Arewa 1%.
"cutarwar kawai ita ce rashin takin
zamani" ...................
ALLAH ya sa mu gane cewa tonon man fetur a yankin
da ba shi da wadataccen ruwan teku yana da babban hatsari. "sannan kuma a
'ka'idar ilimin kimiyya "scientific method" .....kafin a fara drilling
mai sai an samar da mobile refinery (matatar mai ta ko-ta-kwana) don tsaron
lalurar da ka-iya faruwa wadda ba a fata" ire-irensu:-
1. Kwararar shi danyan man (crude oil).
2. 'Barkewar wutar daji wadda mai ke kawowa!
3. Gurbacewar dukkanin rijiyoyin ruwan sha na
gargajiya da na burtsatse da ke yankin da ake tonon man. "da dai
makamantansu"
No comments:
Post a Comment