Monday, 22 August 2016

SAKAMAKON BINCIKE, SABUWAR ADAWA! Daga Sa’idu Bahaushe Dandagoro:

Add caption

Cikin matukar tsinkaye bayan nazari da jin labarai,na zaba tare da banbare bawon gyadar maudu’in sama a jihata don ku mutanenta,da ma masu son ganin kwam ko bibiyar lamurran shugabanci da siyasa a ko’ina suke.

Na zabi hakan ne a karon farko na rubutuna a shafin wannan kafa mai albarka,domin yadda sannu za ta hana zuwa ko kuma tabbatuwar ragayar dutse ajalin mai daki.

Hankali ya dauku matuka kan yadda kwamitin binciken wawurar kudin ‘yan jihar a tsohuwar gwamnati ya gano yadda aka yi ciki da wasu makudan kudade ta hanyar tsarin nan na Sure-P a tsohuwar gwamnatin da ta gabata,wanda dama kowa na tunanin ko tabbatar da walakin goro a miya.
Kamar yadda na gani a labarai an gabatar da hujjoji ingantattu daidaya har guda 28 masu nuna yadda aka yi watanda da kudaden Katsinawa har wuri na gugar wuri  Naira Biliyan 14.3.
Cikin takardun da aka gabatar sun nuna yadda aka ba daidaikun mutane da kungiyoyi,aka kawo jadawalin ayyukan a fili don tabbatarwa daga mai ba Gwamnan Katsina shawara kan kasafin kudi Abdullahi Imam.

Abin takaicin wawurar da aka yi ta nuna hannayen tsofaffin kwamishinonin Kananan Hukumomi da kuma na Kudi da babban Akanta da tsofaffin Shugabannin Kananan Hukumomi da wasunsu kamar yadda aka nuna a rahoton.


Sai dai daga bangaren adawa sun yi suka game da aikin kwamitin binciken tare ma da zargin ba a yi masu adalci.

Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Katsina Yusuf Majigiri, ya nuna Alkalin Kwamitin binciken ya bijiro da batun rikicin Jam’iyyar PDP na kasa wanda ba muhallin yin maganar ba ne nan,sannan kuma kamar kalubalantar rayuwarsa ce ta kashin kansa. Inda kuma ya nuna Gwamnan Katsina mai ci na yin maganganu ga tsohon Gwamnan jihar Katsina da ba su dace ba ko ba su da dadi a wajensu.
Sai dai duk wadannan ba su ne abin mai da hankali a kai ba irin batun zargin da Majigirin ya yi na cewa wannan gwamnatin fa ta Katsina ita ma ce ke da abin fadi a zuwa yanzu,domin a cewarsa ta bata da barnatar da Naira Biliyan 100 ba tare da an ga wani abu a kasa ko ci gaban da ake ta ikirari da hankoron kawowa.

Ni a hangena da nake rubutun nan yanzu shi ne binciken nan yana da kyau,kada a ja layi kada a sassauta a tabbata kuma an yi gaskiya da daidaito kada son rai da zuciya su shigo ciki.
Ku kuma Katsinawa ku bibiyi gwamnatin nan,ku sa ido ku lura da duk motsinta, ta kuma sani in dai bincike ne za a yi iya mata shi kafin ma ta sauka ta hanyar lura da me ke kai wa me ke dawowa!
Wannan kalubale ne ga gwamnati na yi wa mutane bayani da haska masu komai,don kame mutunci da tsayawa kan ra’ayin wadanda take shugabanta.

Mu hadu a wani makon na gaba don mu taba ragayarmu mu ji me ta kunsa kuma,na gode.

Wanda ya rubuta:
Kwamared Kabir Sa’idu Bahaushe Dandagoro
08038387516.
kabeerloquacious77@gmail.com


 Credit: Katsina Post



No comments:

Post a Comment