Kamar yadda kuka sani tsarin biyan albashin ku CONHESS an kirkiro shi musamman saboda ku, sannan dokar ta yi bayani filla filla kan yadda za a rika biyan kudaden alawus da ke cikin wannan tsari.
Amma abin takaici sai aka sukurkutar da tsarin aka karya mashi irli, bukatar da aka so ya ba ita yake biya. An yi amfani da wasu damarmaki marasa dalili ga doka akai ta kara wasu rukunnan ma'aikatan a cikin wannan tsari sannan kuma ba a bin dokar wajen biyan alawus alawus da ta kunsa.
Wannan mummunar hanya da aka dora tsarin akai tana jawo wa al'umma asarar kudade da dama wadanda za a iya amfani dasu wajen kyautata rayuwar al'umma.
Wannan ya sanya Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki matakin dakatar da biyan wadannan alawus domin tantacewa tare da tabbatar da zahirin wadanda wannan tsari CONHESS ya shafa.
Wannan tantancewa za ayi ta ne tare da Shuwagabannin kungiyar kwadago (NLC), kungiyar Ma'aikatan kananan hukumomi (NULGE), kungiyar Ma'aikatan lafiya (MHWUN) da kuma sauran masu ruwa da tsaki a kan wannan al'amari.
Gwamnati tana tabbatar maku da cewa, da zarar an gama wannan tantancewar to za a ci gaba da biyan wannan tsarin CONHESS kamar yadda ya kamata tare da biyan ariyas na tsawon lokacin dakatarwar.
Gwamnati na fatar za kuyi hakuri da wannan dakatarwar ta wucin gadi da akayi.
Bissalam.
No comments:
Post a Comment