Saturday, 9 July 2016

Gov Masari Zai Kafa Hukumar Karba, Kula Da Raba Zakka a Katsina


Gwamnatin Jihar Katsina za ta kafa Hukumar karba, kula da kuma raba Zakka a fadin wannan Jiha.
Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana haka a yayin da ya karbi bakuncin Shuwagabannin kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatissunnah reshen Jihar Katsina.

Gwamnan yace wannan hukuma ita za ta rika amsar Zakka tare da kuma rabata kamar yadda Allah SWT Ya tsara a cikin Al-Qurani Maigirma. Haka nan kuma za a dora ma wannan hukuma alhakin kula da Marayu da kuma gajiyayyu.

Da yake tofa albarkacin bakin shi, Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Alh Aliyu Sabiu Ibrahim Muduru ya ce Majalisar Dokokin ta kammala tantance dokar kafa hukumar kuma za ta gabatar da ita ga Maigirma Gwamna domin samun amincewar shi.


Tun da farko jagoran tawagar kuma Mukaddashin Shugaban kungiyar na jiha Malam Muhammad Sani Daura, ya shaida wa Gwamnan cewa sun kawo wannan ziyara ne kamar yadda aka saba domin yi wa Gwamnan barka da shan ruwa tare da yin addu'o'in neman zaman lafiya da karuwar arziki a wannan Jiha da kuma Kasa baki daya.

Malam Muhammad Aminu Liman Funtua wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar, ya roki Allah da Ya yi wa Shuwagabannin mu jagoranci cikin tsarewa da kiyayewar Shi. Ya kuma yi kira ga al'umma da su kara sa fahimta da hakuri a kan mawuyacin halin da kasar nan take ciki tare da neman sauki daga Allah SWT domin Shi ne kadai mai iko a kan komai.

No comments:

Post a Comment