
Saboda hakan, ‘yan siyasa na amfani da wanna dama
lokacin zabe su furta kalamu masu dadi da yin alkawari daban daban batare da
yin cikakken bincike akan yadda zasu yi tsari akan hanyoyin da zasu bi domin
aiwatar da wadannan aiyuka. shin karancin hangen nesa ne ke hanasu su dobi
hanyoyin daza su samu kudaden da zasu aiwatar da wadannan aiyuka koko basa
tunanin wadansu kalubale dakan iya tasowa na bazata?
Mai girma Gwamna Aminu Bello Masari a yayin da yake
fafatakar yakin cin neman zabe, ya anbaci aiyuka da dama wanda zai yi ma
al’ummar jihar Katsina inda aka zabe shi gwamnan Katsina. Wanda kuma sun cika
mashi alkawarin ta hanyar zaben shi gwamnan Katsina har zuwa 2019.
Toh, Kalubalai kuma tabbas kowace gwamnati na
fuskantar matsaloli da dama wanda sun hada da tabarbarewar arzikin kasa, da
kuma karancin kudade masu shigowa asusun gwamnati.
Wanda a yanzu haka, Gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari na ta fafatakar ganin yadda zata shawo kan matsalolin kananan
hukomomi na jihar Katsina.
Wannan dama wasu dalillai yasa kungiyoyin masu zaman kansu na sakai suka hada duk
alkawarin da mai girma Gwamna Masari yayi ma al’ummar jihar Katsina.
- Binciken faduwar jarabawar ‘yan sakanderi na katsina.
- Duk wani mai rike da mukamin siyasa dole yasa ‘ya’yan shi makarantun gwmanati.
- Karo malaman makaranta da kuma inganta kayan koya karatu.
- Tabbatar da tsaro, rayuka da dukiyoyin talakawa musamman fitinar Fulani masu satar shanu da kuma fitinar Kauraye na cikin gida.
- Inganta wutar lantarki.
- Yin amfani da dam-dam domin samar da ruwan sha, dayin noman rani wajen samar da hanyoyin na dogaru da kai.
- Kaddamar da kamfanoni sarrafa abinci da ma’adanan su. (Food processing companies)
- Duk masu rike da mulki na siyasa zasu rika amfani da asibitoci na gwamnati.
- Aiki tare da Majalisa dokoki ta jiha wajen kaddamar da kundin tsari na ‘yancin yada labari (Information Bill).
- Farfado da mai’aikatar da ke kula da harkukin bada kwangila a bude.
- Bada isassun kayan noma ga ma noma.
- Samar da kwararrun malaman gona wajen inganta noma.
- Rangwame ga manoma wajen siyan kayan noma.
- Bada ‘yanci ga kananan hukomomi wajen sarrafa kudaden su.
- Yin amfani da kayan gida wajen yin aiyuka da ‘yan kwangila zasu yi.
- Bada yanci ga kafafen yada labaru don yin aiki bisa kwarewa.
- Ingantawa da karfafa ma’aikatun gwamnati.
- Kaddamar da masana’antu don samar wa mutane aikin yi.
- Samar da ruwa sha mai tsafta.
- Tsari mai kyau don tafiyar da gwmnati.
- Gwamna da iyalansa baza su zama ‘yan kwangila ba.
- Yin alkawarin aiki da kungiyoyi masu zaman kan su da kuma kwararru wajen tafiyar da gwamnati.
- Taron tattaunawa tsakanin gwamnati da al’ummah.
- Kula na musamman ga ‘yan fansho.
- Tafiyar da gwamnati a bude domin al’umma ta san yadda ake tafiyar da harkoki wanda ya shafe su.
- Gwamnati zata bude kofofin ta domin samun kusanci ga al’umma.
- Ganin inganta tattalin arziki jihar katsina ta hanyar samar da hanyoyin dogaru da kai.
- Karfafa kayan Lafiya a asibitoci da kuma daukar ma’aikatan Lafiya.
- Gwamnati baza ta biya ma jami’an gwamnati kudi wajen siyan magani ko zuwa asibiti.
Kungiyoyin masu zaman kansu ne na jihar Katsina
suka hada wannan zubin alkawari daban daban da Gwamna Masari yayi Kafin hawa
kujerar gwamnan jihar Katsina.
Jama’ar jihar Katsina su tsaya su dubi wannan
aiyuka, shin Gwamna Masari yana saman layi koko ya karkata zuwa wata hanya
daban da ta kaushe ma wadannan alkawurra da yayi.
Shin ayyuka nawa ya fara daga cikin su, nawa aka
kaddamar, da kuma guda nawa ne bai fara ba.?
Gaskiya da sauran aiki agabashi, don aiyukan da aka fara basu kai rabi ba kuma duk an saba ma kaidojin bada kwangila, kamar yadda yayi alkawalin bada kwangila gara ga yan garin to mu anan Daura kwangilar Asibiti Ibrahim Masari ke yinta da Adam yanduna, Bauere. Ta Motel ma ba Dan Daura. Akwai misalai da yawa Amman Dan Allah asuba aygara jar bamu kunya.
ReplyDeleteMuna iya cewa an kamanta a bangarori da dama an Kuma kauce a wasu bangaroriñ.misali maganar yin amfani da dam dam na Jaha wajen Samar da ruwansha anan yayi kokari da wasu fannonin da dama amma maganar bada kwngiloli har yanzu da sakal.
ReplyDelete