Assalamu alaikum warahamullahi wabarakatuh,
Bayan gaisuwa mai cike da girmamawa irinta addinin
Musulinci nayi kokarin rubata wannan wasika ne zuwa ga Malam da nufin yin roko
da jan hakali badan girma na ba a'a saidai don nakasance masoyin Malam kuma
musulmi dan'uwa.
Da farko dai yanda Malam ke shiga al'amurran siyasa
kai tsaye a matsayin shi na uba kuma dattijo mai fada aji! Baya ma al'umma
dayawa dadi kasantuwar babu abinda hakan ke janyowa sai korafe-korafe, zagi da
cin mutunci tare da tuhume-tuhume wasu masu tushe wasu kuma marasa tushe Idan
Malam bai manta ba a lokacin Malam Ummaru Musa Yar'adua ansha jin masallatai
ana gabatar da al-kunut akanshi da salon mulkin shi wanda yake kusan za'a iya
cewa salone iri daya da na Gwamnati mai ci yanzu, duk da dai akwai bambanci mai
yawa domin kuwa Ummaru Musa Yar'adua bai taba hana albashi ba a lokacin azumi
ba.
Ashe idan al-kunut ne wannan Gwamnatin tafi
cancanta ayima wa dan itace al'umma suka sha wahala suka zaba da kansu. Haka a
lokacin Gwamnatin Barr. Ibrahim Shehu Shema sai mukaji Malam yayi shiru yasa
aka daina al-kunut sai gashi wasu na zargin wai anba Malam fili da 10 Millions
inda ya gina 'private secondary school' daga bisani kuma sai naji wasu na
tsegumin wai anba Malam kwagilar sayen motoci shida kanenshi Sabo Musa da kuma
kwagilar ciyarwar azumi a masallatai duk da naji wadannan a matsayin jita-jita
kwatsam saiga Malam na tallata mana Umaru Abdullahi Tsauri (Tata) babu ko
shakka a masallacin G. R. A aka ringa yin wannan hidima ta Tata kowa ya shaida.
Da zaben Shekarar 2015 ya gabato sai kuma mukaji
Malam ya canza akalar campaign dinshi yana cewa APC SAK! duk da dai Umaru
Abdullahi Tsauri yace daf da zabe Shugaba Muhammadu Buhari ne ya tuntubi Malam
ya nemi alfarma ayi masi Masari kuma haka akayi.
Bayan duk wadannan abubuwan sun faru kuma sai shi
zababen Gwamna ya kasa yin aiki kamar yadda ya alkawallanta ma al'umma wajen
yakin neman zabe. Kowa yaji a jikin shi ba sai an fada ba! A ranar sallah data
gabata sai Malam Liman Surajo Katsina yaja hankalin Gwamna da mukarraban shi da
su duba irin yadda mutane ke cikin kunci su kirkira wasu hanyoyin da za'a samu
sauki,yayi jawabai masu gamsarwa. Bayan dan lokaci sai mukaji anata
kalubalantar Malam Surajon dai bayan ainahin gaskiyar zance ya fada.
Wannan ba karamar baka bace ga kungiyar Izalatul
Bidiah wa'ikamatussunah ta jihar katsina idan ku Malamai kuna haka mu kuma fa
yaya kuke tsammanin zamu kasance?
Daga karshe ina roko da jan hankalin ku malamai da
don girman Allah ku tsaya ma gaskiya kadai ba son abin duniya ba. Ba kuma neman
mulki ba, ko wani matsayi a Gwanatance na tabbata wannan matsaloli naku
dayawanmu bamu tare da abinda kuke so a shekaru masu zuwa 2019. Yaa Allah tsare
mana imanin mu, ka cire mana kwadayin abin hannun mutane. Amin
Mansur Halilu 15/07/2016
Allah yasawwake amin
ReplyDeleteAmeen. Siyasa da Addini basa taba haduwa
ReplyDeleteDama aishi gwanine wajen hassada da Neman duniya.
ReplyDeleteAllah yakiyaye Mana imaninmu dana Malaman mu.
ReplyDeleteAmma yakamata Malamai Suqara lura 'yan siyasar Nijeria fa Sunsha Aradun sai sun zubar musu da Mutunci, kamar yanda Suka san Basu da Sauran Mutunci a idon duk wani mai Mutunci.
Akwai abun damuwa Matuqa gaya, Malami yasha gwa-gwar mayar tabbatar da Ingantaccen Addini da Kwatowa Al'ummah haqqinta na Addini da rayuwa kowa yasanshi akan haka, sama da Shekaru 30 Amma aqarshen rayuwa wasu marasa mutunci su rudeshi duk wannan yatafi Abanza.
Duk Wani Abu da Malami Zai Samu Na Shugabanci ko Muqami ko dukiya Wlh baikai darajar Hadisi kwaya daya dazai zauna ya koyawa Al'umma ba.
إنما الأعمال بالخواتيم.
Abunda mutum yacike rayuwarsa akai shine Abun duba da Lura.
Ya Allah ka kubatar damu da Malamammu daka tarkon Shaidan dana miyagun azzalumai Macuta mugwaye da hidqu na 'yan siyasar Qasarmu ta gado.