Tuesday, 19 July 2016

Kira Ga Matasan Katsina akan Majalissar Matasa Katsina- Aminu Ubale

Kamar yadda aka sani da cewa a kwana kin baya an yi taro na kungiyar majalissar matasa dake garin Katsina domin samun matsaya a irin halin da majilisar matasan take a ciki.

Taron an gudanar da shi a Katsina Motel wanda ya samu wakilci daga kungiyoyi masu hannu da shuni akan harkar matasa, sune suka halirci wanna taro. Sannan kuma mai ba Gwamna shawara akan harkokin matasa Ibrahim Khalil ma ya samu wakilci a taron.

Wanda daga karshe bisa dalillai da suka saba wa kundin tsarin majalissar matasa wanda gwamnatin PDP ta karya dokan wajen zaben shuwagabanni majalissar matasan dake nan Katsina.

Da amince war masu hannu da tsaki da kuma wakillan matasa daga kananan hokumomi dake nan jihar Katsina ne suka samu matsiya daya bisa tsarin kundin mulkin Majalissar matasa da wancen gwamnati ta karya doka, a nan take a ka rushe shuwagabanni na bugi da PDP tat aura.

Tare da hadin kai da yawun masu ruwa da tsaki aka sake wani zabe na caretaker wanda zasu shi gaba da jan ragamar mulkin majalissar matasa har zuwa lokacin da za ayi zaben cika guraban gaba daya.

Kwatsam, mun samu labari cewa mai ba Gwamna shawara akan harkar matasa Ibrahim Khalil ya nada sababbin shuwagaban ni na rikon kwarya ta kungiyar majalissar matasa rashen Jihar Katsina.

Zanyi amfani da wannan damar inyi kira ga masu girma shuwagabannin matasa na jihar katsina bisaga sanarwar da aka fitar daga ofishin mai ba gwamna shawara Akan harkar matasa, ta dakatar da shuwagabannin national youth concil of Nigeria. ( NYCN) reshen jihar katsina karkashin jagororin comrade lukman umar kankia. Ni Aminu Ubale Funtua. (financial  secretary ) Sakataren kudi na kungiya a madadin shugaba muna kira ga magoya bayan mu da su yi hakuri gwamnati ta shiga maganar. Duk wanda yaje yayi batanci ko cin mutumci a radio ko social network to bada gwamnati yake fada ba damu yake. Kuma sannan bada yawun muba, saboda mu masu biyyya ne.


Sannan yanzu haka mun fara Magana da jami’an gwamnati akan yadda za’a samu matsaya da fahimta bisa wannan al’amari daya shafi dukkan nin matasan Jihar Katsina gaba daya.

Godiya ga hon sani Aliyu danlami member katsina central,  Alh Haruna Musa SSA Special Duties to Gov Masari. Alh Tanimu Sada Special Assistant to Gov Masari. Hon Aminu Dan Arewa SSA Sport. Alh Shamsu Sule Funtua SSA Special Duties. Dr badamasi lawal SA high education. Alh Sabo Musa chairman da kuma Godiya ga mai girma gwamna Aminu Bello Masari Akan goyon bayanshi da son cigaban matasa.

Daga Karshe ina kira ga matasan jihar Katsina da zamu yi iyakan kokarin mu don ganin cewa ayi abun daya dace wajen tafiyar da Majalissar matasa rashen jihar Katsina, sannan kuma muna iyakan namu kokarin ganin cewa mun hadu da SA Youth Ibrahim Khalil, da duk kungiyoyi masu ruwa da tsaki a wajen ganin cewa an samu mafita bisa wannan matsala d ake faruwa.

Duk yadda ta kaya, zamu fito mu gayama matasan Katsina duk abun da ake ciki. Allah yasa mu dace Ameen.

Aminu Ubale Funtua

Financial Secretary NYCN.

No comments:

Post a Comment