Gwamna Aminu Bello Masari ya rantsar da Alhaji Tanimu Audi Bindawa a matsayin wakili a Majalisar zartaswa ta Jiha kuma Kwamishinan kula da harkokin Addini.
Bayan kammala rantsuwar, Gwamnan yayi kira gare shi da yasa tsoron Allah a duk abinda zai yi domin gobe kiyama Allah zai tambaye shi. Ya kuma hore shi da kada ya kawo ko saka banbancin akida a cikin aikin shi.
Gwamna Masari yayi mashi addu'ar Allah Yayi mashi jagoranci kuma Ya bashi ikon amsa duk tambayar da za ayi mashi gobe kiyama a kan wannan aiki da zai yi.
Source: SSA Social Media To Gov Masari
No comments:
Post a Comment