A
taron ta na goma sha ukku (13) da ya gudana a dakin taro dake Gidan Janar
Muhammadu Buhari, fadar Gwamnatin jihar Katsina, Majalisar zartaswa ta jiha a
karkashin jagorancin Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari, ta amince da bukatar
da Hukumar Tsaron Kasa (Directorate of State Security Service) ta gabatar mata,
ta bude Makarantar Sakandare a nan jihar.
Makarantar wadda za ta kasance makamanciyar irinta ta Hukumar
'Yan Sanda da take a garin Mani, an tanadar mata Matsugunni a Makarantar Sakandaren koyon kimiyya ta Gwamnati da ke a
garin Musawa. Kuma da zarar an kammala shirye shiryen da suka kamata za a fitar
da cikakken bayani musamman ta bangaren hanyar Shiga Makarantar da kuma inda
daliban dake cikin Makarantar za su koma.
Haka
nan kuma, Majalisar ta karbi rahotannin wucin gadi na tantance Ma'aikatan
kananan hukumomi kashi na farko da na biyu, kuma da zarar an kammala hada
rahoton za a kafa Kwamitocin sauraren koken wadanda abin ya shafa domin
tabbatar da adalci.
Majalisar
ta kuma amince da bukatar tantance Ma'aikatan da suke aiki a matsayin
'kwantaragi' (Contract), wannan zai sanya a tantance sahihancin yawansu, aikin
da suke yi da kuma yanayin yarjejiniyar daukar su aikin da suke akai.
Asali: SSA Social Media
No comments:
Post a Comment