Tuesday, 26 July 2016

Jiga-jigan PDP Ta Katsina State Sun Kai Ziyarar Ta'aziya A Gidan Eng. Musa Nashuni

"PDP KATSINA STATE HEAD QUARTERS"
Shuwagabannin Jama'iyyar PDP na Jihar Katsina karkashin Jagorancin Hon Salisu Yusuf Majigiri Mashi, Sunjema Dantakarar Gwabnan Jihar Katsina a karkashin tutar Jama'iyyar PDP a Zaben 2015 Ta'aziyya a Yau ENGR MUSA NASHUNI a KAFINDANGI karamar hukumar Kankia, bisa ga Rasuwar (Sarakuwarsa Haj KARIMA) Mahaifiyar Uwar Gidansa Haj Binta Nashuni.

Tafiyar ta hada da Tshohon kakakin majalisar dokoki na Jihar Katsina Hon Ya'u Umar Gwajojo. Yayi addu'a Allah ya gafarta mata zunubanta, Allah yasa aljanna tazama makomarta.


Mai Girma Shugaban Jam'iyyar PDP Hon Salisu Yusuf Majigiri Mashi yayima marigayar addu'ar neman gafara ga Allah SWT, ya Kuma sake ba iyalanta hakuri da sujere da rashin da sukayi nata. Domin dukkan wani mahalicci sai ya ansa kiran Ubangijinsa Allah.

Ya Kuma Sake addu'ar Kara nemama kasarmu Nigeria zaman Lafiya da kwanciyar hankali tare da nemama talakkawa samun mafita na halin da kasarmu tasamu kanta a yau.
Asali daga 
Abubakar Shafi'i Alolo

No comments:

Post a Comment