Tuesday, 26 July 2016

ANYA IMANINMU ZAIYI SAURA KUWA? Daga Ameer Mahmud Dan'amarya

Allah ya halicci dan adam yasa mashi tausayi da jinƙai, abinda akecema dan'adamtaka, adabi'ar dan adam tunda can muna da tausai yajunanmu, hattana da kwarin dabbobi dan adam na tausayinsu a dabi'ance da addinance.

Mu musulmai tausayi da jin kai na daga cikin alamu da cikar imani  na mutum, amma fa a yanzu ta canja zani domin sammm bahaka bane musamman matasanmu da manya masu budurwar zuciya babu sauran dan adamtaka atare dasu, kokari nasamar ma da social media labari yasa sam bama tausayi ko jin kai ga yan'uwanmu ma bare kuma dabbobin dake rayuwa atare damu.

Zakaga mutane suna daukar hotonsu selfie da matattu na hadari ko wata mutuwa  wadda yakamata su tausaya amma sam tunanin neman like na friends yasa zukatansu sun shagaltu da aikin duniya basa tuna inda wadannan dasuka mutu suka tafi wanda ba makawa suma zasuje yanzu, yau, gobe ko jibi
, a'a wannan baya gabansu ya salaaam Allah kashiryar damu.
Zakaga mutane nadaukar hoto suna sallah tagaban liman mutane sun maida komai abin talla hatta da addininmu da ibadarmu, gaskiyar magana munsaki layi muna kokarin zama sokaye wawaye marasa tausai jin kai da duk wata alama dazata gwada mu mutane ne masu sanin yakamata da tunanin gobe, munzama kauyawa gidadawa  dasunan wayewa .

Yakamata mufarka mudawo cikin hayyacinmu dan wannan sam yasaba ma dabi'ar dan adam, raka mamatanmu da wayoyi muna daukar hoto maimakon jimami dayimasu adduar dacewa da masauki mekyau da nema masu gafara agurin Allah.

Da haka nake kira ga al'umma dasuji tsoron Allah aduk kan al'amuranmu na yau da kullum, Allah yasa mudace da rabo me amfani.

Allahu aalam 
Wabillahi taufeeq

26-07-2016

No comments:

Post a Comment