
Yin hakan ya faru ne don yadda gwamnati katsina ta
shiga wani hali na rashin kudade dake shigowa asusun gwamnati. Wannan tsari a
lokacin jama’ar jihar Katsina sun yaba mashi bisa wannan tunani da kuma nufin za aiwatar da aikin.
[decision].
To a lokacin kuma akwai wadansu sace na jama’ar jihar Katsina wanda sun yi
korafi a kan cewa, akwai banbanci tsakanin niyar aikatar [decision] da aiki da
kuma fara aiwatar da wannan aikin,[implementation] ganin yadda kamun ludayin
wannan gwamnati shine ta iya yin Magana mai zaqi, gwanin dade kamar duka kenan,
amma aiwatar da aikin [full implementation] da abun da suka ce shine babban
maqiyinsu a yanayi irin mulkinsu.
Yanzu haka an share watanni fiye da wata shadda [6]
amma har yanzu gwamnatin bata dauki damarar fara aiwatar da wannan tsari
[policy] na amsar haraji ga masu irin sanao’in da na zayyana a baya.
Wani abun al’ajabi shine irin yadda gwamnatin
Masari ta duqufa wajen ranto kudin bashi da ruwa [interest] wanda yanzu haka
majalisar dukoki ta jihar Katsina sun kara bashi dama don cin bashin Naira
biliyan sha hudu [N14 Billion]. Jama’a ku sani fa, duk bashin da gwamnati ta ci
to tana sadaukar da rayuwar mu ne da na ‘yayan mu wajen samun sakewa da walwala a nan gaba, [Liquidating our future].
Domin idan ba a samu hanyoyi wanda za su kawu ma
jihar Katsina kudi ba, to gwamnati dole ta shi gaba da cin bashi don tafiyar da
aiyukan gwamnati, sannan duk wanda ya amshi mulki nan gaba, ba zai iya aiwatar
da komai be sai dai biyan bashi ga jama’a na wahala matukar wahala.
Shi hangen nesa yana da kyau, idan baka da fasahar
hangen nesa to za ka iya dauko kwararru wanda sun shahara wajen hangen nesa da
tsare-tsare wanda zai taimaki jihar Katsina.
Wannan yaskiya ne ya kamata gwamna ya duba Irin mutanen da ya ke ba mukamai.
ReplyDeleteHaka dai yakamata, domin za'a shiga wani hali idan ba'a gyara ba
ReplyDelete