Saturday, 2 July 2016

Cliqq Magazine Ta Samu Ganawa Da Mansur Ali [SA Radio Monitoring]


Cliqqmagazinehausa.blogspot.com ta samu gannawa ta wayan cellular da sabon Mai taimaka Gwamna Masari akan harkokin Radio Mansur Ali.

A inda ya bayyana ma Cliqqmagazinehausa.blogspot.com irin ayyukan da suka shafi aikin shi wanda ya hada da wayar wa mutane kai tare da ilmantar da su halin da gwmanati ta ke ciki. Sannan ya kara da cewa mutanen dake  zaune a qauyuka basu da hanyar samun labarai sai ta kafan Gidan Radio, wanda ya zama wajibi a isar masu da sakon alkairai da gwamnatin Masari ke yi.

Ya kara da cewa ganin yadda ba kowa ke jin yaran turanshi, ya kamata a fassara masu irin sabbin tsare-tsare da gwamnati ki aiwatar wa domin suma su fahimta su bada nasu gudunmuwa ko kuma koke.


Mansur Ali Mashi ya kara da cewa akwai gangami da wayar ma al’umma kai akan safarar Kwaya da shan miyagun kwayoyi da al’umma ke fama dashi wanda duka suna cikin irin aiyukan da ke karkashin ofishin shi.

Mansur ya yi alqawarin ciga sako sako don yada manufofin gwmnatin Masari harma kauyukan Fulani wanda da ba sujin hausa ma duka za’a rika wayar masu da kai da kuma ilimantar da su akan yanda zasu an fana da gwamnatin Masari da kuma hanyoyin da za su bi wajen miqa koken su zuwa gwamnati.



Follow Our twitter handle: @Cliqq_Magazine
Like Our Facebook Page: Cliqq Magazine
Email: cliqqmagazine.@gmail.com
Blog Address: Cliqqmagazine.blogspot.com

Tel No: 08062883759
Please share your thoughts in the comment box below

No comments:

Post a Comment