Friday, 15 July 2016

BUĎADĎIYAR WASIKA ZUWA GA SHEIKH Yakubu Musa Hassan -Mansur Halilu

Assalamu alaikum warahamullahi wabarakatuh,

Bayan gaisuwa mai cike da girmamawa irinta addinin Musulinci nayi kokarin rubata wannan wasika ne zuwa ga Malam da nufin yin roko da jan hakali badan girma na ba a'a saidai don nakasance masoyin Malam kuma musulmi dan'uwa.

Da farko dai yanda Malam ke shiga al'amurran siyasa kai tsaye a matsayin shi na uba kuma dattijo mai fada aji! Baya ma al'umma dayawa dadi kasantuwar babu abinda hakan ke janyowa sai korafe-korafe, zagi da cin mutunci tare da tuhume-tuhume wasu masu tushe wasu kuma marasa tushe Idan Malam bai manta ba a lokacin Malam Ummaru Musa Yar'adua ansha jin masallatai ana gabatar da al-kunut akanshi da salon mulkin shi wanda yake kusan za'a iya cewa salone iri daya da na Gwamnati mai ci yanzu, duk da dai akwai bambanci mai yawa domin kuwa Ummaru Musa Yar'adua bai taba hana albashi ba a lokacin azumi ba.

Ashe idan al-kunut ne wannan Gwamnatin tafi cancanta ayima wa dan itace al'umma suka sha wahala suka zaba da kansu. Haka a lokacin Gwamnatin Barr. Ibrahim Shehu Shema sai mukaji Malam yayi shiru yasa aka daina al-kunut sai gashi wasu na zargin wai anba Malam fili da 10 Millions inda ya gina 'private secondary school' daga bisani kuma sai naji wasu na tsegumin wai anba Malam kwagilar sayen motoci shida kanenshi Sabo Musa da kuma kwagilar ciyarwar azumi a masallatai duk da naji wadannan a matsayin jita-jita kwatsam saiga Malam na tallata mana Umaru Abdullahi Tsauri (Tata) babu ko shakka a masallacin G. R. A aka ringa yin wannan hidima ta Tata kowa ya shaida.


Da zaben Shekarar 2015 ya gabato sai kuma mukaji Malam ya canza akalar campaign dinshi yana cewa APC SAK! duk da dai Umaru Abdullahi Tsauri yace daf da zabe Shugaba Muhammadu Buhari ne ya tuntubi Malam ya nemi alfarma ayi masi Masari kuma haka akayi.

Bayan duk wadannan abubuwan sun faru kuma sai shi zababen Gwamna ya kasa yin aiki kamar yadda ya alkawallanta ma al'umma wajen yakin neman zabe. Kowa yaji a jikin shi ba sai an fada ba! A ranar sallah data gabata sai Malam Liman Surajo Katsina yaja hankalin Gwamna da mukarraban shi da su duba irin yadda mutane ke cikin kunci su kirkira wasu hanyoyin da za'a samu sauki,yayi jawabai masu gamsarwa. Bayan dan lokaci sai mukaji anata kalubalantar Malam Surajon dai bayan ainahin gaskiyar zance ya fada.

Wannan ba karamar baka bace ga kungiyar Izalatul Bidiah wa'ikamatussunah ta jihar katsina idan ku Malamai kuna haka mu kuma fa yaya kuke tsammanin zamu kasance?

Daga karshe ina roko da jan hankalin ku malamai da don girman Allah ku tsaya ma gaskiya kadai ba son abin duniya ba. Ba kuma neman mulki ba, ko wani matsayi a Gwanatance na tabbata wannan matsaloli naku dayawanmu bamu tare da abinda kuke so a shekaru masu zuwa 2019. Yaa Allah tsare mana imanin mu, ka cire mana kwadayin abin hannun mutane. Amin

Mansur Halilu 15/07/2016

4 comments:

  1. Ameen. Siyasa da Addini basa taba haduwa

    ReplyDelete
  2. Dama aishi gwanine wajen hassada da Neman duniya.

    ReplyDelete
  3. Allah yakiyaye Mana imaninmu dana Malaman mu.

    Amma yakamata Malamai Suqara lura 'yan siyasar Nijeria fa Sunsha Aradun sai sun zubar musu da Mutunci, kamar yanda Suka san Basu da Sauran Mutunci a idon duk wani mai Mutunci.

    Akwai abun damuwa Matuqa gaya, Malami yasha gwa-gwar mayar tabbatar da Ingantaccen Addini da Kwatowa Al'ummah haqqinta na Addini da rayuwa kowa yasanshi akan haka, sama da Shekaru 30 Amma aqarshen rayuwa wasu marasa mutunci su rudeshi duk wannan yatafi Abanza.

    Duk Wani Abu da Malami Zai Samu Na Shugabanci ko Muqami ko dukiya Wlh baikai darajar Hadisi kwaya daya dazai zauna ya koyawa Al'umma ba.

    إنما الأعمال بالخواتيم.

    Abunda mutum yacike rayuwarsa akai shine Abun duba da Lura.

    Ya Allah ka kubatar damu da Malamammu daka tarkon Shaidan dana miyagun azzalumai Macuta mugwaye da hidqu na 'yan siyasar Qasarmu ta gado.

    ReplyDelete