Monday, 25 July 2016

AIKI MAIKYAU ALOKACI MARA AMFANI (RABON TAKIN GOMNATIN MASARI) BY Ameer Mahmud Dan'amarya

Dukkan yabo da godiya su tabbata ga allahu maqagina mamallakin dukkan komai.

Kasan cewar tattalin arzikin nigeria yashiga wani hali sakamakon fadowar danyen mai akasuwar duniya ta danyen mai,  da kuma ta'addanci yan naija delta wanda yajawo koma baya aduk harkokin dasuka shafi tattalin arzikin kasarmu nigeria. Wannan yasa amatakin tarayya da jahohi musamman na arewa suka maida hankali kasokan kan farfado da harkar noma dan samar da abinci da kudin shiga ga kasa da jahohi baki daya, saboda kowa yafahimci dogaro da mai bazai haifar ma kasar nan da ɗa mai ido ba.

Adalilin haka gomnati tayi yunkurin tallafa ma manoma, dan cimma wancan ƙuduri na sama, amma banan gizo ke saƙar ba musamman mu anan katsina.

Tun cikin rani gomnatin katsina da sa hannun gomnatin tarayya suke yayata bada tallafin noman shinkafa, amma yazuwa yanzu da shinkafin masu halin shuka shinkafa r batare da jiran gawon shanun tallafin gomnati ba ke kulla ciki,banga kojin labarin wannan gomnati anan katsina tabada tallafin naira daya ba, tahaɗa mu faɗa da talakawan da aka ansamma kuɗin buɗe ƙungiyar noman shinkafa.

Ɓayan wancan alƙawalin gizo da aƙai mana na noman shinkafa, tun azamanin gomnatin yanbfamilƴ anɗ frienɗs (pɗp) abune sababbe ana bada taki akan lokaci a katsina lokacin fara shuka da lokacin tiri (banƙasa) sau biyu a damina, amma haryanzu taki baizo hannun manoma ba, wanda nasan dun wanda keleƙa gonaki yaga wadansu Ma sungama sama masararsu taki harda zurare sungama,


Amma yanzu ne wannan gomnati kekokarin wai bada taki a katsina, ninasan dunk wanda ke karkara yasan wannan taki da za'a bada inma akwai amfani to dankaɗan ne, koma ince bashi da amfani ga manoma ayanzu domin dun wanda kenoma nasan kusan kadanne suka rage basuyi tiri ba kuma suma sungama sayen takinsu.
Da haka muke ganin anya wancan ƙuduri na sama na samar da wadataccen abinci da kaucewa dogaro da danyen mai zai cika kuwa?

Labarin tallafa ma noman nan da gomnatin keta yekuwa to inaga a office ake wancan noma mukam manoma bamu ga ko balama ba.

Da haka nake kira ga gomnati tasake ɗaurin zaninta, wajen harkar noman nan gaskiya batai komai ba, haryanzu muna ma gomnatin katsina kyakkyawan zaton zasu dawo kanhanya inda suka saki layi, shiyasa bama gajiyawa wajen bada shawara koya take dan ciyar da jaharmu gaba da fita kunyar jamaa ga gomnatin damu muka zabeta.

NA DUƘE TSOHON CINIKI, KOWA YAZO DUNIYA KAI YATARAS.
Allah yaɗaukaka jahar katsina
Allah kasama noman mu albarka


No comments:

Post a Comment