Tuesday, 7 June 2016

Sanata Madawaki Ya dauki nauyin horas Da Matasa 800 Ilimin Komputa A Yankin Daura Zone


Matasa maza da mata dari takwas ne da suka fito daga lungu da sako na Daura zone suka kammala bitar horaswa ta sati takwas akan ilmin komputer a fadin Daura zone wanda sanatan Daura zone Engr. Mustapha Bukar ya shirya kuma ya dauki nauyi. wannan bitar horaswa ta matakin Diploma akan ilmin computer anyita ne a santoci goma sha uku a kananan hukumomi goma sha biyu na Daura zone karkashin kulawar komitin da sanatan ya nada.

Kamfanin ICT Global plus ne Sanata Engr Mustapha Bukar ya bawa kwangilar bada wannan horo wanda a halin yanzu haka suka samu nasarar kammala wannan shiri.matasan da suka samu damar kasancewa cikin wannan shiri sun bada cikakken hadin kai ga malamai da ma'aikatan wannan kamfani. Kusan dukkanin matasa da suka samu wannan horo sun nuna jin dadi tareda godiya dangane da wannan shiri da sanatan nasu ya kirkiro masu.

A zantawar da jaridar cliqqmagazinehausa.blogspot.com tayi da daya daga cikin yan komitin kula da wannan shiri Hon. Shehu Abdu Daura ya ambata cewa shidai wannan shiri Sanata Engr. Mustapha Bukar ya kirkiro shine don cika wasu daga cikin alkawula da ya dauka a yayin kamfe na 2015 ga al'ummar Daura zone, ya kara da cewa ganin yadda wannan bangare na ilmin komfuta yake da muhimmaci ga rayuwar al'umma ta yau da kullun ne dalilin da yasa sanata ya bawa wannan bangare muhimmanci ya kara da cewa a lokacin bukin yayewa tareda bada takardar shaidar kammala wannan bita ne sanata yayi alkawalin bawa kowane dalibi tallafi don ya samu damar aiwatar da ilmin da yasamu ga al'ummar wannan yanki. 



Ya furta cewar akwai wasu shirye shirye makamantan wannan da sanatan ke shirin sake aiwatarwa nan bada dadewa ba a shiyyar ta Daura zone don amfanin musamman matasa don ganin an rage yawan masu zaman kashe wando

No comments:

Post a Comment