Na tabbatar idan zamu cire son zuciya, ba zamu iya cewa shema a Katsina bayyi komai ba, ko dukkan ayyukan da yayi na banza ne, babu masu amfani. Hasali ma, duk da na yarda akwai son zuciya a cikin ayyuka da dama, amma ayyukanshi da dama suna kan hanyar data dace, kuma ayyuka ne da zasu kawo cigaba mai dorewa a jihar Katsina wadanda idan gwamnatin data gaje shi ta dora bisa wadannan ayyuka, tabbas zasu amfanar da jama’a matuka.
Kamfanonin taki a Jihar Katsina
Misali, ayyukan gina kamfanonin taki a Jihar Katsina. Wadannan kamfanonin murza takin zamani da Gwamna shema ya kafa a lokacin shi, hakika mataki ne mai kyau da zai kawo cigaba kwarai musamman a fannin aikin gona, samar da ayyukan yi da arziki mai dorewa. A yau, fuskar tattalin arzikin Nigeria ta juya zuwa alkiblar Noma da ma’adanai, wanda sune suka fi tabbas a cikin ko wane irin yanayi. Inganta aikin gona yana bukatar takin zamani, ingantaccen irin shuka, magungunan kwari da horar da manoman akan sababbin hanyoyin noma na zamani da amfani da kayayyakin noman.
Tarakatoci sama da 350
A lokacin shema, ya samar da tarakatoci sama da 350 ga manoman Jihar Katsina. Duk da wadannan Tarakatoci an saka son zuciya wurin rabonsu, an baiwa mutanen da ba zasuyi amfani dasu bane sun sayar, amma har yanzu Naga akwai sauran irin wadannan tarakatocin suna jibge a KATARDA quarters suna ta lalalcewa babu mai amfani dasu.
Federal University Dutsinma (Agriculture)
A cikin zamani gwamnatin shema, daya daga muhimman dalilai da yasan Gwamna ya rook Alfarmar Kafa Jami’ar Tarayya ta Dutsinma (Akan fannin Gona) shine ta yadda za’a horar da yayanmu hanyoyin zami na inganta nomad a kiwo. DUk da abubuwa da yawa sun faru akan Jami’ar, amma hakan bai cire amfaninta ga al’umma ba, idan akayi amfani da ita yadda ya dace. Tabbas, Jami’ar zata taimaki al’ummar jihar Katsina musamman ta bangaren ilimin aikin gona na zamni.
Songhai Farm
Shema ya kafa Gonar Zamani ta Songhai Farm Dutsinma, wannan gona an kafa ta ne musamman don ta zama wurin reno da gwajin sababbin hanyoyin noma na zamani da inganta irin shuka, dabbobi da tsuntsaye. Gonar kuma zata zama wurin bada horo na musamman ga matasa akan sababbin dubarun inganta nomad a kiwo. Gonar, irinta ce farko a duk fadin Nigeria. DUk da ita ma gonar akwai korafe-korafe masu yawa akanta, amma tabbas amfaninta nada yawa ga al’ummar jihar Katsina wurin samar da kudaden shiga, inganta aikin gonad a kiwo, samar da sana’oi da rage rashin ayyukanyi.
Saidai, wani abin takaici, dukkan wadannan abubuwa dana lissafa a sama, wadanda suke da matukar Muhimmanci wajen inganta aikin gonad a kiwo, wanda shine asalin abinda arzikin Nigeria, Jihar Katsina dama duniya baki daya ya dogara akanshi, dukkansu sun tsaya cik! Basu aiki, sai kadan, wadansu suma aikinsu, ya canza ma’ana, ba akan cimma burin da aka kafasu suke ba.
A gani na, idan Mai Girma Gwamna zai dogara akan wannan kadai, da nufin inganta noma, ta hanyar farfado dasu su koma aiki yadda ya kamata, babu shakka Jihar Katsina zata amfana.
Duk da nasan Mashawartan Maigirma Gwamna, kan iya kallon farfado da wadancen ayyukan kamar farfado da martabar gwamnatin data gabata ne, saboda haka gwara a barsu su lalace. Wannan idan akwai masu irin wannan tunanin, babu shakka shawarar banza ce, gurguwa da bata nufin alkhairi ga mai girma gwamna. Shawara ta gari itace, a matsayin daya samu Kanshi, yayi iyakar kokarinshi don tabbtar da Kudaden al’ummar Jihar Katsina da akayi amfani dasu don yin wadancen ayyukan basu tafi a banza ba, an inganta su, al’umma da gwamnati taci amfaninsu.
Sako zuwa ga Abdulhadi Ahmed Bawa, Aliyu Sabiu Muduru, Abubakar Yahya Kusada, Abdullahi I. Mahuta don yin abinda ya dace.
Ma’assalam!
No comments:
Post a Comment