Gwamnatin jihar katsina a yunkurin ta na inganta harkokin kiwo yanzu haka tayi hadaka da babban bankin Nigeria tayi tanadin wasu awaki na musamman don rabawa Mata makiyaya bashi.
Sudai wannan awaki suna haihuwa ne sau biyu a shekara kuma suna haihuwar yan biyu biyu ko fiye da haka sannan suna samar da nono sosai akalla lita daya a kowace rana.wannan ne ya bawa gwamnati sha'awa ganin yadda wannan sana'a zata kawo ma makiyayanta alfanu da dama.Yanzu haka ma dai wannan dabbobi na can a killace a hannu malaman dabbobi na ma'aikatar gona ta jihar katsina suna samun kula yadda yakamata kafin a mika su ga makiyaya.
Shidai wannan bashi kamar yadda cliqqmagazinehausa.blogspot.com ta samo labari duk wanda aka bawa bashin wannan akuya to ba da kudi ne zai biya ba a'a zai biya ne da akuya kamar yadda akabashi akuya.
Wannan salon da gwamnati ta dauka na inganta kiwo mutane da dama sunyi marhabin dashi ganin yadda kiwon yana daga cikin arzukin da wannan jiha ke tunkaho dashi amma anyi masa rikon sakainar kashi.
No comments:
Post a Comment