Wannan matsala ta biyo bayan makeken gibin da yake tsakanin kudin da suka samu a watan Mayun daga asusun rabon kudi na kasa, wanda a wannan watan sun sami Naira Bilyan Biyu ba Milyan Dari Hudu da Saba’in da Tara (N2.479B), alhali kuwa abinda ake bukata a biya albashin da sauran abubuwan da suka zama dole irin su Fansho da makamantan su shi ne Naira Bilyan Ukku da Milyan Dari Bakwai (N3.7B).
A halin yanzu, babu wata karamar hukuma da za ta iya biyan albashin ma’aikatan ta da abinda yake shigo mata.
Ita kanta Gwamnatin Jiha abinda ta samu bai kai abinda ake bukata ayi albashin ba sai da aka cika Miliyan Tamanin da Takwas (N88M) daga asusun ajiya na jiha sannan aka sami yin albashin.
Abinda wannan alkalumma ke nunawa shi ne, kananan hukumomin jihar nan basu da isassun kudin da za su iya biya masu albashi har sai an yi cikon gibin sama da Naira Milyan Dubu Daya (N1B) wanda ita kanta Gwamnatin Jihar ba ta dasu.
Kuma dama tun kafin yanzun, Gwamnatin jiha ce take daukar nauyin cike gibin da ake ta samu a watannin baya wajen biyan albashin kananan hukumomin wanda ya zuwa watan Afrilu, Gwamnatin jiha ta cika wa kananan hukumomi sama da Naira Bilyan Hudu (N4B) wajen biyan albashin daga asusun ta.
Wannan ya wajabta a sake bin kadin yawa da kuma yadda ma’aikatan kananan hukumomin suke, dalilin haka ne yasa aka yanke shawarar biyan kudin albashin a hannu (Table payment).
Sakamakon tabbacin samun ma’aikatan bogi a cikin kananan hukumomi, Gwamnatin jihar Katsina, a watannin baya tasa aka yi wani aikin tantance ma’aikatan wanda a karshe aka sami sama da mutum Dari Takwas (800) wadanda basu zo gaban Kwamitin tantancewar ba.
Bayan wannan kuma sai aka gano akwai wasu ma’aikatan lafiya sama da Sittin (60) da suke amsar albashin Gwamnati alhalin kuma suna aiki a wasu wurare daban inda kuma suke amsar albashi karshen ko wane wata.
Ta wannan biyan albashin a hannu da aka fara ne aka gano cewa akwai mutane da yawa wadanda suke amsar albashi amma kuma basu aikin domin suna zaune ne a wasu jihohin dabam suna wata hidimar, wasu ma a kasashen waje suke da zama iyaka duk wata suji albashi ya shiga subi su kwashe.
Kuma duk wannan almundahanar ba wai gamagarin mutane bane ke yin ta, a’a, manyan mutane ne kuma sanannu a kananan hukumomin na su suka daure wa abin gindi, domin kuwa kusan duk ahalin su ne ake samu da irin wadannan halayen.
A yanzu haka akwai karamar hukumar da aka gano wani tsohon shugaban karamar hukumar yana da ma’aikata har guda ashirin da ukku (23) da suke amsar albashi amma hidimar shi kawai suke yi domin har da masu aiki a gidan gonar shi da makamantan su. A kuma wannan karamar hukumar aka gano cewa akwai mutane Ashirin da Tara (29) da wasu sun yi ritaya daga aiki wasu kuma sun ma rasu amma ana ci gaba da amsar albashin su sama da shekara biyar. A nan ne kuma aka sami Malaman da basu ma san sunan makarantar da aka ce suke koyarwa ba ballantana su san Hedimasta ko wani abokin aiki.
Akwai karamar hukumar da aka taras tana da wani mukami mai suna “file tracer” kuma har guda Hamsin da Biyu (52) suke da su, baya ga Direbobi Hamsin (50) da kuma ma’aikatan ofis a LEA guda Dari Biyu da Tamanin da Daya (281) kwatankwacin yawan malaman wata karamar hukumar.
A bangaren Lafiya (Health) da kuma bangaren Ilmi da Walwalar jama’a (ESD) nan ma abin ba kyawun gani domin z aka iske ma’aikacin da abinda ya hada shi da asibiti amma duk wani alawus na ma’aikatan asibiti yana amsar shi a cikin albashin shi, sannan su kan su ma’aikatan lafiyar duk wani alawus da ya shafi aikin asibiti suna amsar shi duk kuwa da cewa sun san ba haka ya kamata ba.
Duba ga wannan yanayi da ake ciki ya zama wajibi ga Gwamnati, ba don ta kuntata wa kowa ba, a ci gaba da wannan biyan kudi na hannu (Table payment) da ake yi tare da dakatar da biyan duk wani alawus da ya shafi ma’aikatan asibiti har sai an tantance sahihanin wadanda suke ma’aikata na gaske da kuma wadanda suka cancanci a basu wadannan alawus alawus din.
Gwamnati ta kuma yanke shawarar canza tsarin yadda ake yin albashin; daga yanzu, shuwagabannin yanki (Unit Heads) ne za su rika tantance ma’aikatan su tare da shirya albashin su a duk wata, ta yadda duk idan aka sami matsala an san wanda za a kama da laifi, kuma wannan tsarin zai taimaka wajen ciwo kan halin rashin da’a da rashin girmama na gaba a tsakanin ma’aikata.
Shuwagabannin kungiyar likitoci ta kasa (NMA), kungiyar ma’aikatan unguwar zoma (NNMA), kungiyar ma’aikatan lafiya (MHWUN) da kuma na kungiyar kwadago (NLC) duk za a shigo da su cikin aikin tantancewar domin tabbatar da anyi wa kowa adalci.
===================================================
Wannan bayanin shi ne makasudin taron da Gwamna Aminu Bello Masari yayi da Masu ruwa da tsaki na wannan jiha wanda suka hada da Masu Martaba Sarakunan Katsina da Daura, Alhaji AbdulMumini Kabir Usman da kuma Alhaji Umar Faruq Umar, tsofaffin Gwamnoni, tsofaffin manyan ma’aikatan Gwamnati, Manyan Malamai daga bangarori daban daban, ‘yan kasuwa da kuma ‘yan siyasa.
Mahalarta wannan taro sun yaba tare da jinjina ma wannan Gwamnati a kan yadda ta tsare biyan albashi tare da gudanar ayyukan ci gaban kasa, sabanin yadda wasu jihohi suka kwashe watanni babu albashi.
Sun shawarci Gwamnati da ta rika yin hukunci a kan duk wanda aka kama da laifi domin ya zama darasi ga saura. Sun kuma bada shawarwari da dama a kan yadda za a ciwo kan wannan matsaloli musamman ta bangaren habaka kudin shiga, tare da nuna goyon bayan su a kan wannan mataki na tantance ma’aikata.
To ina kudin da federal allocation ta bada daga may2015 zuwa june 2016 gran naira billion 88
ReplyDelete