Wednesday, 8 June 2016

#GUZURIN_RAMADANA: Mu Ciyar da Abinci 'yan Najeriya.-Muhammad Ali Mansur

                                
Babu shakka ciyarwa aikine babba daga cikin ayyukan lada wadanda Allah ya tabbatar dasu acikin addinimu na musulunci. Zamu fahimci hakan a yayin da ciyarwa ta kasance daya daga cikin ayyukan da ake gabatarwa a matsayin kaffara kamar yanda bayanin yazo acikin wasu ayoyin Al-qur'ani mai-girma.


Hakika Allah shine yake fifita wasu ayyuka akan wasu, kamar yanda ya fifita dan-adam akan sauran halittu, ya fifita daren lailatul-kadari akan sauran darare, ya fifita ranar Juma'a akan sauran ranaku, yaku ma dai fifita watan #Ramadan akan sauran watanni don hakanema galibin ayyukan ibada sukafi yawan falala da tarin lada acikin wannan watan na Ramadana. Akan hakanema yasanya dayawa daga cikin magabata sukayi magan-ganu da ma wallafe-wallafe akan tarin falalar dake acikin ciyar da abinci a irin wannan watan, don haka nima naga dacewar in tunatar damu da wani abu daga cikin dan  abunda na tsinkaya acikin wannan sha'ani, dafatan Allah ya datar damu baki daya.
Ciyar-da-Abinci; Shine bayar da dukkan wani nau'in abinci ko abun-sha da aka sarrafa ko kuma wanda ba'a sarrafaba ga mabukaci, haka kuma bayar da abun da za'a iya sayen/mallakar abincin shima nau'ine daga cikin na'ukan ciyarwar.


Lallai Ubangijinmu Allah acikin littafinSHI mai tsarki ya tabbatar mamu da cewa; zai jarrabemu da wani abu na daga #Tsoro da #Yunwa da #Talauci da #Tawayar_dukiya... har zuwa dai fadrSA;  "ka yima masu hakuri bushara, sune wadanda idan musiba ta samesu suke cewa; Daga Allah muke kuma zuwa gareshine makomarmu take."

Najeriya; a nan kuma dukkan wanda a halin yanzu yake a cikin kasar Najeria zai fahimci cewa 'yan-Najeriya suna cikin Jarabawa ta tsananin #Yunwa da #Talauci da #Tawayar-arziki, wanda bayan munyi hakuri mun maida lamurranmu zuwaga Allah to fa muna da bukatar sashenmu ya ciyar da sashe, don dama yana daga cikin hikimar Allah da ya sanya wasunmu mawadata wasu kuma mabukata dan ya jarrabi kowannenmu dafatan kuma Allah yabamu ikon yin nasara akan wannan jarabawar.

Babu shakka acikin jerin ayyukan neman lada da ake gabatarwa a cikin wannan watan mai tarin albarka babu wani aiki da ya fi fifiko da yawan falala fiye da ciyar da abinci (hatta zuwa Umara), to kuma musamman acikin irin wannan mawuyacin halin damuke cikinshi a Najeriya ayau. Lallai magabata basa wasa da ciyarwa a irin wannan yanayin domin; an ruwaito cewa wata rana Abdullahi bin Mubarak ya fito da guzurinshi zaya tafi aikin hajji sai ya yada zango a wani gari, yana zaune yana hutawa sai yaga wata mata ta fito ta dauki wani mushen kaza a cikin shara ta shiga gida da ita, sai yabi diddiki har yasamu isa gareta ya tambayeta akai sai tace yanayine ya tsananta agaresu ta yadda basu da wani zabi illa cin wannan mushen, anan take Abdullahi bin Mubarak ya basu dukkan guzurin da yafito dashi shikuma ya koma gida yace ai wannan ciyarwar itace aikin hajjin nashi, sai gashi kuwa wadanda sukaje aikin hajji a shekarar sun dawo suna labarta mashi cewa sunji ana yekuwa anafadin sunanshi akan yayi aikin hajji karbabbiya...Allahu Akbar. Haka kuma an ruwaito cewa Abdullahi Ibn Umar RA. Idan yayi azumi baya buda-baki sai tare da miskinai, haka ma dai Hasanul-Basari ya kasance yana shiryama masu azumi kayan buda-baki kuma yana kai-da-kawo lokacin da suke buda-bakin domin ya tabbar da komai yana tafiya daidai. Hammad Ibn Sulaiman shima ya kasance yana shirya kayan buda-baki na mutum hamsin a kowace rana a Ramadan, Kaza-lika ma Imamu Ahmad ya taba yin azumi bayada abin buda-baki sai waina daya amma ya bayar da ita ga wani wanda yafishi bukata. Allahu Akbar
 

'Yan-uwa hakafa abun yake a wasu sassa na duniya misali; a kasar Sudan, wani dan-uwa yana bamu labarin cewa; idan ka sake lokacin shan-ruwa ya rutsa dakai akan hanya tofa ko kafi tsoho gardama masu ciyarwar bazasu barka ka isa gidankaba zasu tareka ala tilas sai sun ciyar dakai abnincin buda-baki, haka ma a Qatar, Kuwait da Saudi-Arabiya a inda kamfani guda zaiyi baje kolin dukkan kayan abincin da yakeyi na tsawon watan Ramadanan a kyauta, ko kuma wasu mutane su saye dukkan abincin da gidajen dafa abinci keyi don arika rabama mutane kyauta har watan ya kare, kai ta kaiga har fastoci ake likawa masu dauke da jaddawalin nau'ukan abincin da za'a ciyar dakai idan kaje, kai in takaice maku zancen, akwai inda har kyaututtuka suke bayarwa wasu ma harda kudi idan kaje, su dai bukatarsu kawai kaje kaci abinci. Allahu Akbar. To 'yan-uwana 'yan-Najeriya shin wai mu bamu da bukatar irin abunda mutanennan suke nemane? Shin sunfimu son Al-jannarne? Ko kuwa sunfimu yakinine akan falalar Ramadanan? To shikenan mukuma bazamuyi wani katabusba gwar-gwadon halinmu? Ya-Salaaam...

Musanifa duk wannan kokarin nasu sunayine domin neman dacewa da kuma samun falalar nan ta mai-ciyar-da-abinci musamman a irin wannan watan, kamar dai yanda yazo a nassoshi da dama misali; Annabi SAW yace: Duk wanda ya ciyar da mai azumi za'abashi lada kwatankwacin irin ta mai azumin da yaciyar din batare da anragema wanda ya ciyar din ladar tashiba. Sannan yace; ciyar da abinci yana daga cikin ayyukan da ke sanyawa ashiga Al-janna salin-alin (cikin aminci). Kuma fa mu sani Annabi SAW yace: ita Sadaka (ciyarwa) bata rage komai acikin dukiya.., domin duk abunda ka ciyar sai anbaka madadinshi kamar yanda yazo a wani hadisin inda Annabi SAW yace; A kullum wasu Mala'iku guda biyu suna safka sai daya daga cikinsu ya rika cewa; ya Allah ka mayema duk mai ciyarwa, sai kuma dayan yace; ya Allah kaba mai kamewa (wanda-baya ciyarwa) talauci.

Abun-lura: Musanifa ba Lallai sai gwamnatoci ko Manyan Attajirai ko 'yan-kasuwa koma 'yan-siyasa ne kadai za su iya ciyarwarnan ba, domin dayawa wadanda suke ciyarwar a Sudan da sauran kasashen da muka lissafa matsakaitan mutanene irina irinku galibi ma asusu sukeyi tsawon shekara ko kuma suyi hadaka da tarayya sai su shirya ciyarwar, don haka mumafa lokaci bai kure mamuba ko ayanzunma muna iya farawa gwargwadon iya abunda Allah ya hore mamu kai koda acikin kasonmune na abincin buda-bakin kamar yadda aka ruwaito Aisha RA tayi a wani lokaci tana Azumi sai wata mabukaciya ta nemi abinci a wurinta a lokacin duk gidanta dabino ukkune take dashi amma saboda sanin mahimmancin ciyarwa da kuma tausayi ga mabukaci ta bata dukkan dabinon nan guda ukkun, sai gashi cikin ikon Allah kafin rana ta fadi sai da Allah yakawo mata wani bawan Allah ya aiko mata da abunda tayi buda-bakin dashi. Allahu Akbar, kunga dai duk mai ciyarwa Allah yana maye mashi abinda ya ciyar din ko? To lallai sai mu fadaka mu jajirce mu daure mu cije mufara wannan aikin na ciyar-da-abinci daga yanzu gwar-gwadon ikonmu dafatan Allah ya bamu ikon.

Daga Karshe nike kara dai rufe wa da jawo hankalinmu akan cewa bamu da tabbacin idan zamu sake samun damar kaiwa ga wani Ramadanan mai zuwa, don haka yanzune akeyi ba sai anjiraba dafatan Allah yabamu ikon fin karfin zukatanmu ya kuma cire mana rowa ya tsarkake mana zukatanmu daga riya. Allah yabamu ikon azumtar wannan watan Ramadanan muna masu Imani da neman Lada ya kuma datar damu da dukkan Alkhairan da ke cikinsa yasa muga karshensa Lafiya ya karbi dukkan ibadunmu da zamu gabatar acikinsa.
#Asha_Ruwa_Lafiya...

Muhammad Ali Mansur
Maihulakt08@yahoo.com


No comments:

Post a Comment