Tuesday, 7 June 2016

Barawo Yayi Kisan Kai a Daran Farko Na Azumi A Katsina

  

A daren jiya ne Litinin 6/6/2016 wadda tazo dai dai da daya ga watan Ramadan hijra ta 1437 da misalin Karfe biyu na dare wani Yaro mai suna Abdulaziz da ake ma lakani da Kunkuru ya dira gidan wani Yaro makwabcinsa mai suna Yusha'u Aliyu dukkansu mazauna Unguwar Kofar bai dake cikin garin Katsina da niyyar yi masa sata .


Lokacin da Shigar masa yayi ihu barawo da niyyar neman dauki nan take ya daka masa wuka a qirji ya kashe shi ya jefa shi a ramin masai ya kwashe wayoyinsa da kudi , Wanda a halin yanzu ana neman yaron da yayi kisan.


Don haka Muna roqon jama'a Wanda ya ganshi ko yaji labarinsa da ya sanar da Hukuma mafi kusa . hoton yaron dake da dorowar rigar shine Wanda yayi kisan a gefe gudan gawar Wanda aka kashen ne.

Da fatan Allah ya gafarta masa ya shirya mana zuriya ya bamu mafita ga wannan lamari.

No comments:

Post a Comment