Saturday, 11 June 2016

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNATIN JAHAR KATSINA- Comrade Dalhat Usd Danja

Assalamu Alaikum bayan gaisuwa da fatan Alheri, Ya Aiki ya zaman Office Allah yabaka ikon cika Alkawarin daka Daukarma Al'ummarka Allah kuma ya kara taimaka wannan Gwamnatin .

Batare da bata lokaci ba zanyi Amfani da wannan Damar Domin baka shawara akan wadansu Al'amura dasuka shafi Tafiyar da Mulkinka da sauran Hidindimun Gwamnati Yallabai Shawarwarina Sune Kamar Haka: .

1. Yallabai Ina ganin daza'a Daga screening din Ma'aikata da Akeyi zuwa Wata nagaba wannan watan Abama kowa Albashin shi Domin samun Saukin Rayuwa .

2. Kamata yayi screening din adunga yinshi Ministry by Ministry yanda Al'umma bazasu takura Sosai ba .

3. Yakamata ka dunga zagayawa kanajin koken mutane bawai komai a kawo maka office ba .

4.Dukkan Policy da gwamnati zata Dauka yakamata ta duba Consquencies nashi kafin tayi Implementing .

5. Dukkan lokacin da za'a samu tsaikon Albashi yakamata gwamnati ta fito tayima Al'umma bayani Saboda suyi tanaji har lokacin dazasu samu Albashi .

6. Yakamata gwamnati ta daina biyan Ma'aikatan Jaha Albashi idan har Na local government bazasu samu nasu ba A dunga hadawa ana biyansu tare! .


Daga karshe ina kira hade da rokon Wannan gwamnatin data taimaka ta biya Ma'aikata Albashinsu kosa samu suyi Azumi cikin jindadi da walwala! .

Comrade Dalhat Usd Danja 11-06-2016

No comments:

Post a Comment