Saturday, 30 April 2016

Gina Shaguna a Bakin Stadium Na Daura Zai Bata Tsarin Tsawira Na Birane- Shamsuddin Salisu Daura



Wannan tunani bai yi daidai ba, maimakon gwamnati ta karfafa dokokin ta na tsarin taswira birane, ta kuma kwato irin wannan wurare da azzalumai suka handame a baya, shine za a mana kamzon kuruge da revenue.
Muddin aka maida wannan wurin kasuwa to za a Kawo cunkoso da bata taswira ta gari.
Munga abinda wasu gwamnatoci suka yi wajen kwato filaye na makarantu da maaikatu da aka sace.

Hasali ma wannan sauran filin anyi shine domin ayi parking motoci idan ana wasa ko wani taro, Amma duk da haka yayi kadan.



Bayan haka akwai transahara Road dualisation wanda anyi survey kusan shekara goma da suka wuce daga Kano zuwa Zinder.

Shawara ta a nan tunda wannan zamanin Canji ne, gwamnati ta Kwato filayen ta daga hannun azzalumai Gwamnati ta ka karfafa dokokin ta kan handame filayen maaikatun gwamnati.

A hukunta Wadanda aka hada baki da su a baya aka aikata wannan barna.
Sai kuma gwammati ta sayi filaye a wuraren kasuwanci ta Gina shaguna domin neman revenue.

Ko kuma aje gaban karakanda stadium a Gina shaguna domin a hana encroachment.
Wani abin mamaki ma wai ma aikatan Kupda ne suka bada shawara Bayan duk da su a kayi barna a baya.


Allah ya kyauta

1 comment:

  1. Gaskiya ne Shamsu,Allah sanya gwamnati ta dauki shawararka.

    ReplyDelete