Friday, 22 April 2016

Yanda Wasu 'Yan Naigeriya Ke Tara Dumbin Dukiya ta Hanyar Wahalar da Talakawa ke ciki - Ahmad Isyaku Katsina

A lokacin da 'Yan Naijeriya ke fama da zingar ciwon tabarbarewar tattalin arziki da kuma karancin man-fetur da kasar ke fuskanta, tabarbarewar tattalin arzikin wanda daya biyo baya sakamakon faduwar farashin man-fetur warwas a kasuwar duniya da kuma faduwar darajar naira wacce ta durkusawa dalar Amirka da darajarta ke hauhawa , wasu 'yan kasuwa a kasar sun zabi su gina shekarsu ta jin dadi da tara dukiya ta hanyar kumbura farashin kayan abinci dana wasu amfanin gida fiye da gona da iri, koda kau yanayin ta ake ciki na tsadar kayan bai shafi wasu kayan ba. Wasu kuma daga cikin 'yan kasuwan da tsadar kayan ta shafi kasuwancinsu, sunyi kama da masu maraba da yanayin marar dadi , domin kuwa kakarsu ta yanke saka, a inda suke fakewa da labaran-dola-tayi-sama su ci karensu ba babbaka, wato su hauda farashin kaya ko aiki sama, linki-ba-linki ta yanda zasu sami riba mai tsoka, samun kudi cikin sauki ba tare da wata zufa ba. Wato wata sabuwar hanya ce ta tara dumbin dukiya da ta bullo musu - tsuntsu daga sama gassashe. Zaka ji wani lokacin suna korafi a baki cewa aikinsu ko kasuwancinsu zai durkushe idan har wannan yanayi na narkewar tattalin arziki ya cigaba a kasar to amma a zukatansu sun san ba haka bane. Basa fatan wannan yanayi na wahala ya kare don gudun romon ribar da suke kwasa ya kare.


A wannan yanayi mai wahalar gaske ga 'yan Naigeriya wanda ya kamata ace suna nuna tausayi, ragi, hakuri da soyayya ga juna, abin takaicine ganin irin yanda wasu 'yan kasuwa suka maida talaka saniyar tatsa. Kadan ne daga cikin 'yan kasuwar ke nuna tausayi da ragi. Ko shakka babu gaskiya ne cewa farashin kayan masurufi dana wasu abubuwa ya karu a Naigeriya , kuma wasu yan kasuwan na bakin kokarinsu da nuna tausayi wajen taimakawa jama'a domin samun sauki kuma gaskiya ne cewa wasu daga cikin 'yan kasuwan, kasuwancinsu bazai iya jure wuyar da ake ciki ba idan har wannan hali da ake ciki ya cigaba tsawon lokaci, to amma kuma ba karya bane cewa da yawa daga cikin 'yan kasuwan zasu iya taimakawa wajen rage wahalhalun da talakawa suke ciki idan suna nuna kishin kasa da tausayin talaka. Kwanaki mun samu rahoton cewa wani dan kasuwa dake a jihar Kano yayi kira ga 'yan kasuwa 'yan uwansa da suji tsoron Allah su tausayawa jama'a inda ya bayyana cewa ba kowani kayan amfani bane tsadar kayayyakin ta shafa ba, to amma wasu daga cikin 'yan kasuwa nayin amfani da damar cewa dola tayi tsada su kuntatama jama'a. Zan bada misali da farashin ruwan leda, hakika farashin kudin leda ya karu sosai kusan linki biyu.

A kwanakin baya ne bada dadewa ba, wata kungiyar 'yan kasuwa masu siyar da ruwan-sha na leda da akafi sani da 'fiyo wota' suka hadu kuma suka yanke shawarar kara farashin kudin ruwa daga N50 zuwa N70 ko N80 duk jaka daya. Wani rahoto daya biyo bayan kammala tattamnawarsu akan karin farashin shine, wani daga cikin 'yan kasuwan a kungiyar bai lamince da karin farashin ba, inda ya bayyana cewa zai cigaba da siyar da ruwan shan akan tsohon farashi. Shin tambaya anan itace, shin kyauta yake samar da ruwan kuma bai cin riba ko kadan? Koko hakuri yake da ribar da yake samu marar yawa wacce a da mai dumbin yawa ce kafin hauhawar farashin leda wacce ake siyowa daga kasashen waje domin sarrafa ruwan cikin leda? Ni a iyakar sani na da tunani na hakurine yake da riba marar yawa ba don wai baya samun riba ba ko kadan. A ra'ayina da tunani yana da tausayi da kishin kasa.


A takaice, abinda ke faruwa a halin yanzu shine , jakar ledar fiyo wota daya ana siyar da ita ne akan N100 yanzu a jihar Katsina abinda bai taba faruwa ba abaya. Abin takaici shine 'Yan Naijeriya sun kasance suna labartawa juna da korafi akan yanda cin hanci da rashawa ke so ya latata kasar da juyayi akan yanda wasu manyan jami'an gwamnati na kasar ke cika aljihunsu da dukiyar al'umma su bar talakawa cikin wahala da talauci to amma abin mamaki shine , wasu 'Yan Naigeriya sunyi kama da wa'anda suka manta da halin da irin wadannan 'yan kasuwa masu zuciyar dutse suke kokarin jefa su. Ya kamata shuwagabannin addinai, hukumomin gwamnati da masu zaman kansu su dage da maida hankali wajen fadakar da mutane akan tausayi, soyayya da kishin kasa . Ya kamata ace 'yan Naijeriya su rungumi juna da tausayi a irin wannan yanayi na wahala. Haka kuma ya kamata gwamnatin kasar ta sake kara linka kokarinta da zage damtse wajen ganin wannan yanayi na wahala da ake ciki an wayi gari ya gushe kuma talakawa na murmushi kamar yanda tayi alkawari.

No comments:

Post a Comment