Rahoto daga Abdulmumin Sabo
A yau ne 22/04/2016 mai girma Gwamna
jihar Katsina Rt Hon. Aminu Bello Masari ya zanta da yan jarida na jihar
katsina a kan
nasarorin ayyuka day ake gudanar tun daga hawanshi mulki.
Cliqqmagazinehausa.blogspot.com ta samu
wannan labari daga shafin yanar gizo na mai ba gwaman shawara akan harkokin
hanyoyi na sadarwa a yanar gizo watau Abdulhadi Ahmad Bawa
“Batutuwan da Mai girma gwamnan jihar
katsina Rt Hon. Aminu Bello Masari yayi karin haske akansu lokacin tattaunawar
sa da yan jarida yau juma'a 22/04/2016 a gidan gwamnati.
- Muna cigaba da samawa mutanen cikin
garuruwan Daura da Malumfashi ruwan famfo
-Mun bada kwangilar gyara madatsar ruwa
ta Ajiwa don ganin ta cigaba da aikin ta na samar da lita miliyan sha daya ga
garin katsina da kewayenta
-Shirye Shirye yayi nisa game da ganin
an kammala aikin garin katsina tareda garuruwan kafin soli Kankia da kuma Charanci
isasshe Kuma tsaftataccen ruwan sha daga babbar madatsar ruwa ta Zobe dam.
Wannan aiki zai samawa kananan hukumomi bakwai ruwan sha.
-Muna gyare gyare da sabbin gine gine a
wasu daga cikin makarantun da muke dasu da dama a fadin jiha
-Muna gyarawa tare da daukaka darajar
asibitocin dake a garuruwan Daura katsina da Funtua
-Mun kashe kudi Naira miliyan dari da
ashirin da takwas don daukar likitoci da wasu kwararrun ma'aikatan lafiya
-Cikin hukuncin Allah mun inganta tsaro
da zaman lafiya musamman yadda muka samu nasarar murkushe masu satar shanu
-A shirye mu ke muba kowane dan jiha hakkinsa
kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada amma baza mu lamunci wuce gona da iri
ba.
No comments:
Post a Comment