A ranar Asabar 23-04-2016, mai girma Gwamna RT. Hon
Aminu Bello
Masari yayi tattaunawa daya saba yi duk bayan lokaci kadan, A taron wanda ya
kunshi manufar wanda yake kunshe da bayanai da bayyana ma al’umar yadda
gwamnati ke sarrafa kudin d ake shigowa da kuma kuma yadda ake kashe wadannan
kudade.
Haka zalika, ya bayyana ma al’umah irin ayyuka na
Alheri daya ke yi, sannan kuma bayyana irin tsare tsare na ayyuka da gwmantin
shi ta tanada za tayi ma al’umma.
To amma wani hanzari ba gudu ba, shin ko mai girma
Gwamna Masari yana yi ma al’umma a wajen yin taron bayanin dalillai da yasa ya
bada da umurni ga masu aikata gyran makarantu na gwamnati a kana nan hukumomi
da ke Batagarwa da Ajiwa da a fadada ajin
karatu wanda zai dauki dalibai dari da hamsin (150).
Abun tambaya a nan shine, shin wannan tsari yayi
dai dai ga tsarin da ya da ce da zuba dalibai a aji? Koko tayaya Malami zai
koyar da dalibai guda 150 kuma su fahimta, su gane cikin natsuwa abun da malami
yake koyawa? Shin ko su wa ke ba mai
girma Gwamna shawara akan wannan fanni?
Abu na biyu shine, shin ko mai girma Gwamna Masari
yakan yi bayyana gamsas she ga al’ummah wajen hanyoyi daya tsara domin kawo ma
jihar Katsina kudade ta hanyoyi daban daban. Domin jama’a sun ciga damuwa akan
irin halin da matsala da za’a fuskanta
idan ba an samu wata hanya mafi a’ala kuma mai yuwowa da za a bijiru
domin samun kudade.
Allah ya
taimaki gwamnatin jihar Katsina.
No comments:
Post a Comment