A duk
lokacin da aka sami canjin Gwamnati to tabbas sabuwar Gwamnati za ta gaji
dumbin abubuwa daga tsohuwar Gwamnati, kama
tun daga hakkokin ma'aikata (albashi, fansho, garatuti, karin girma da sauran
su), ayyukan da aka kammala, wadanda aka fara amma ba a kammala ba sai kuma
wadanda aka ce za ayi amma ba a fara ba.
A nan
Jihar mu ta Katsina ma haka abin ya wakana.
Da
yardar Allah, za mu bi wadannan abubuwa sannu kan hankali, daya bayan daya,
domin sanin halin da wannan Gwamnati a karkashin jagorancin Dallatun Katsina,
Alhaji Aminu Bello Masari ta taras da wadannan abubuwa sannan kuma muyi bayanin
irin kokarin da tayi wajen ta kai dauki yadda kamata, duk kuwa da matsi na na
karancin kudin shiga da ake fuskanta.
BANGAREN
SAMAR DA RUWAN SHA (Kashi na Daya)
A bisa
ga halin da matatun ruwa na Jihar suke ciki a daidai lokacin da wannan Gwamnati
ta kama aiki, a iya cewa ba su taba shiga cikin mummunan yanayi irin haka ba,
domin kuwa rahoton da Ma'aikatar ruwa ta Jiha ta bayar ya nuna cewa babu wata
matatar ruwa da take samar da abinda ya kai rabin abin da ya kamata ta samar.
Duk
kuwa da cewa ko da suna aiki yadda ya kamata ba za su iya cimma bukatun al'umma
ba wanda a yanzu ya kai kimanin lita 120 a kan kowane mutum. Dududu abinda suke
samarwa a manyan garuruwan jihar bai kai kashi goma cikin dari (10%) ba.
Daga
cikin matsakaitun ma'aikatun ruwa guda arba'in da daya (41) da ke a fadin
Jihar, wadanda aka taras suna aiki basu kai kashi Ashirin cikin Dari (20%) ba.
Sannan
kuma rashin tsayayyenamfani da kishi ya sa mafi yawancin ma'aikatun ruwa na
karkara sun zama basu da wani amfani.
Tsarin
samar da ruwa na birane ya kumshi garuruwan Katsina, Daura, Funtua, Dutsinma,
Malumfashi da Jibia. Dukkan wadannan garuruwa, ban da Daura, suna samun ruwa ne
daga madatsun ruwa (Dams) da ke a wannan Jiha, ita kuwa Daura an yi mata tsarin
amfani da rijiyoyi ne (borehole).
Ma'aikatar
ruwa ta garin Daura ta share sama da shekaru Hudu (4) ba ta aiki, ita kuwa ta
Malumfashi ta yi sama da shekaru Bakwai (7) bata motsa ba.
Saboda
tsufa da lalacewar kayan aiki, ma'aikatar ruwa ta Ajiwa wadda kuma ita ce take
birnin Katsina da kewaye ruwa tana samar da kasa da kashi Sittin (60%) na
abinda ya kamata ta samar.
Saboda
karancin wutar lantarki da kuma man Disel da kananan hukumomin su ke bayarwa,
Ma'aikatar ruwa ta Jibia tana aikin awa Shidda (6) a rana ita kuma Dutsinma
tana awa (8). Ita kuma Funtua tana yin aiki na awa Goma sha Biyar (15) a rana
idan akwai wutar lantarki daga kamfanin Wuyar.
A
karshen tattaunawar da Gwamna Masari yayi da jami'an Ma'aikatar ruwa ta Jihar,
ya bada umurnin a kawo mashi lissafin adadin kudin da ake bukata domin gyaran
ma'aikatun ruwa na Daura da Malumfashi, domin wadannan garuruwa su ci gaba da
samun ruwa ba tare da bata lokaci ba.
A
cikin watan sha daya na shekarar da ta gabata (November 2015) aka kammala aikin
gyaran ruwa na garin Daura wanda yaci kimanin Naira Miliyan Talatin Talatin da
Hudu, kuma Alhamdu lillah, yanzu a duk rana garin Daura yana samun a kalla Lita
miliyan biyu da rabi na ruwa a duk rana ta Allah.
A halin
da ake ciki kuma yanzu, aikin da aka bada na ma'aikatan ruwa na garin
Malumfashi da aka bada kan kudi Naira Miliyan Dari da Arba'in da Daya shi ma ya
kammala, domin tuni ruwa ya samu a garin Malumfashi.
A
cikin kwana Dari da hawan Gwamna Masari aka gyara matsakaitan ma'aikatun samar
da ruwa na Rahamawa Abattoir, Dutsin Safe da kuma Sabuwar Unguwa duka a nan
cikin garin Katsina.
Zancen
kuma da ake yanzu, Gwamnati ta bada aikin gyaran Ma'aikatar ruwa ta Ajiwa wanda
ya hada harda matatar ruwan, wannan zai sanya ta rika samar da ruwa kamar
asalin yadda aka tsara ta tun farkon kafa ta. Wannan aiki za a yi shi a kan kudi Naira Bilyan Daya da Miliyan Dari Tara (N1.9b).
Famfunan
samar da ruwa masu amfani da hasken rana guda Sittin da Hudu (64) da kuma na
tukajihaa-tuka guda Dari da Biyu (102) aka gyara a yankuna daban daban na
wannan jiha.
Mu
hadu a kashi na Biyu in shaa Allah
No comments:
Post a Comment