Thursday, 21 April 2016

Na Gama Duk Wani Shiri Don Gina Kananan Asibitoci ukku (3) a Kananan Hukumomin Daura Sandamu da Mai'adua Da Nake Wakilta-Hon Sani Fago


hata labari daga Abdulmumin Sabo

A tattaunawar data gudana tsakanin cliqqmagazine.blogspot.com da Rt. Hon. Sani Sa'idu Fago dan majalisa mai wakiltar Daura Sandamu da Mai'aduai ya ambata irin tanade tanade da ya kudirta aiwatarma al'ummar da yake wakilta don ganin sun samu saukin rayuwa

1)      Bangaren lafiya: Dan majalissar ya ambata cewar ya gama duk wani shiri don gina kananan asibitoci uku a kananan hukumomin Daura Sandamu da Mai'adua da yake wakilta wanda a cewarsa zai wadata su da isassun kayan aiki don ganin al'ummar da yake wakilta sun samu sauki.

2)      Fannin ilmin computer:
Anan ma Dan majalissar ya fadi cewar ya gama shiri tsaf don ganin ya gina dakin koyon ilmin computer musamman in akayi la'akari da yadda wannan ilmin keda muhimmanci a rayuwar yau da kullun. Haka kuma ya kara da cewa Wannan daki za'ayi amfani dashi wajen horar da yara masu shirin rubutu jarabawar SSCE da JAMB da post UME ganin yadda wannan ilmi keda tasiri a wadannan Jarabawowin.


3)      Samar da Ruwan Sha: akwai tsarin da tuni mun gama akan cewa zamu gina borehole a kwauyuka domin samara da ‘yan gantarce rowan sha.

4)      Rage rashin aikinyi a tsakanin al'ummar da yake wakilta: A wannan bangaren ma Dan majalissar ya fadi cewar yayi tanadin koya ma matasa maza da Mata har dari biyar 500 sana'oi tare da basu tallafin da ya hada da kekunan dinki babura yar kurkura (keke napep) da sauransu.

Duka wannan ababen more rayuwar zai aiwatar dasu ne da zaran budget na wannan shekara 2016 ya fara aikinyi.




No comments:

Post a Comment