Wednesday, 27 April 2016

Gina Shaguna Da Gwamnati Zatayi A Gaban Stadium Na Garin Daura Zai Janyo Mata Alfanu Da Dama

Mallam Abdullahi Habu
A kokarinta na tattalawa tare da kirkiro sababbin hanyoyin da zasu rika kawo ma jiha karin kudin shiga komin kankantarsu yasa gwamnati  ta yanke shawarar gina shaguna a gaban stadium dake a garin Daura kamar yadda Kwamishinan wasanni Jin dadin matasa da raya karkara na jihar Katsina Mallam Abdullahi Habu Dankum ya shaidawa cliqqmagazinehausa.blogspot.com

Kwamishinan ya kara da cewa hukumar tsaftace muhalli SEPA tare da hadin gwiwar hukumar KUPDA suka yi la'akari da yadda a yanzu haka wasu daga cikin masu sana'a tuni sun fara mamaye wannan wuri hakan yasa suka ga gina shaguna zai zama alfanu ga gwamnati musamman yadda zata rika karbar kudin haya kuma ta anshi revenue sannan kuma wurin shima zai samu bunkasa bugu da kari kuma ya kawo karshen mamaye wurin da masu sana'a yan kama wuri zauna suke cikin yi a halin yanzu.

Halin ko in kular da gwamnati ta nuna da barinsa sakaka gashi kuma fuskar kasuwa ya haifar da janyo hankalin wasu masu sana'ar hannun kamar kanikanci masu wankin mota masu walda da sauran su tuni suka fara baje hajarsu ba tare da wata sahihiyar shaida ba daga hukumar dake da alhakin basu iznin yin hakan

Kafin fara wannan gini sai da hukumomin SEPA da KUPDA suka yi nazarin duba yiwuwa ko rashin yiwuwar gina shaguna a wannan wuri wanda  daga karshe suka amince kuma sukaba gwamnati tsari da kuma yadda taswirar wannan shaguna zasu kasance.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa da zaran an kammala gina wannan shaguna gwamnati zata bada su haya ga yan kasuwa masu bukatar yin kasuwanci a wannan wuri. Ya kara da jaddada cewa wannan gwamnati bata da niyyar maimata irin kwamacalar data rika faruwa a baya dangane da mallakawa wasu ko wani filin gwamnati maimakon hakan sai dai ita gwamnati ta rika amfani dashi ta yadda zai amfani al'umma


Ta Fannin jama'ar gari kafin fitar wannan bayanin na Kwamishina saboda rashin samun sahihancin yadda lamarin yake dayawa na shakkun wannan al'amarin gina shaguna da gwamnatin jiha zata yi a gaban stadium saboda ganin yadda gwamnatocin da suka shude suka rika mallakawa mutane wurare makamantan wannan wanda a cewarsu yin hakan bai masu dadi ba. Ra'ayoyin mafi yawancin mutanen garin Daura ya nuna suna gudun yar gidan jiya ma'ana suna gudun kada daga baya kuma itama wannan gwamnati ta dauki salon mallakawa wasu shafaffu da mai daga cikin yan siyasa tata.

Hada rohoto : Abdulmumin Sabo

2 comments:

  1. Wannan tunani bai yi daidai ba, maimakon gwamnati ta karfafa dokokin ta na tsarin taswira birane, ta kuma kwato irin wannan wurare da azzalumai suka handame a baya, shine za a mana kamzon kuruge da revenue.
    Muddin aka maida wannan wurin kasuwa to za a Kawo cunkoso da bata taswira ta gari.
    Munga abinda wasu gwamnatoci suka yi wajen kwato filaye na makarantu da maaikatu da aka sace.
    Hasali ma wannan sauran filin anyi shine domin ayi parking motoci idan ana wasa ko wani taro, Amma duk da haka yayi kadan.
    Bayan haka akwai transahara Road dualisation wanda anyi survey kusan shekara goma da suka wuce daga Kano zuwa Zinder.
    Shawara ta a nan tunda wannan zamanin Canji ne, gwamnati ta Kwato filayen ta daga hannun azzalumai
    Gwamnati ta ka karfafa dokokin ta kan handame filayen maaikatun gwamnati.
    A hukunta Wadanda aka hada baki da su a baya aka aikata wannan barna.
    Sai kuma gwammati ta sayi filaye a wuraren kasuwanci ta Gina shaguna domin neman revenue.
    Ko kuma aje gaban karakanda stadium a Gina shaguna domin a hana encroachment.
    Wani abin mamaki ma wai ma aikatan Kupda ne suka bada shawara Bayan duk da su a kayi barna a baya.
    Allah ya kyauta

    ReplyDelete