Sunday, 25 November 2018

Obasanjo, Jonathan, Kwankwaso sun halarci nadin sarautar Atiku



 A yaune ake nadin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar sarautar Wazirin Adamawa, manyan mutane daga sassan kasarnan daban-daban na halartar taron a Adamawa.



Haka kuma a yaune Atikun ya cika shekaru 72 a Duniya.




Daga cikin wadanda suke halartar taron akwai tsaffin shuwagabannin kasa, Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauransu.

PMT ta ruwaito cewa, Obasanjo ya yabi Atiku sosai kuma ya tabbar da cewa, idan ya zama shugaban kasa zai ba marada da kunya.


No comments:

Post a Comment