Monday, 24 September 2018

Sakacinmu ne ya janyo mana matsala a Osun- Lai Mohammed


Minsitan watsa labaran Najeriya, Lai Mohammed, ya ce sakacin jam'iyyarsa ce ta sa bata yi nasar kai tsaye a zaben gwamnan da aka yi a jihar Osun ranar Asabar ba.

Da yake zantawa da BBC, ministan ya ce APC din ta yi sakaci ne saboda tana tunanin cewar ba ta da matsala a jihar Osun.


Mohammed ya ce amma tun da dai lamarin ya kasance haka, jam'iyyar za ta sake shiri game da yadda za ta tunkari abin da ya saura a zaben da ke tafe.

Ya ce APC za ta tattara kan magoya bayanta don su fito kwansu da kwarkwatansu a zaben da ke gaba.

Duk da cewa akwai matsalolin da jam'iyyar ta gani game da zaben, Mohammed ya ce sun amince da sakamakon zaben yadda yake a halin yanzu.
Ya ce jam'iyyarsa ba ta fargabar tunkarar abin da ya saura a zaben, amma APC ba za ta bayyana dabarun da take shiryawa ba.

A ranar Lahadi ne dai hukumar zabe ta INEC ta ayyana zaben gwamnan jihar Osun a matsayin wani zaben da ba a kammala ba.

Babban jami'in hukumar INEC a zaben farfesa, Adeola Fuwape, ya ayyana zaben a matsayin wanda ba a kammala ba ne don ratar da ke tsakanin 'yan takarar da ke kan gaba bai kai adadin kuri'un da aka soke ba.

An soke kuri'u 3,498 a zaben bisa dalilai na sace akwatin zabe da kuma batan-dabon jami'in hukumar INEC yayin da dan takarar jam'iyyar PDP ya fi dan takarar APC da kuri'u 353 kawai.

Nan gaba ne dai hukumar INEC za ta bayyana ranar da za a sake zabe wasu mazabun da ak soke kuri'u cikin wasu kananan hukumomin jihar.

No comments:

Post a Comment