Thursday, 6 September 2018

Kungiyar yan kasuwa dake karkashin Dahiru Mangal ne suka sayi wa Gwamna Masari fom


Kungiyar Yan kasuwa jihar Katsina a karkashin Alhaji Lawal Dahiru Mangal sun saya wa gwamna Aminu Masari fom na tsayawar takara a matsayin gwamnan jihar Katsina.

Wakilin mu ya shaida mana cewa Gwamna Masari ne kawai zai tsaya takarar Gwamna a jam’iyar su, amma sauran kujerun tun daga kujerar Sanata, ‘Yanmajalissun Taraiyya da na jaha sai anyi masu zaben fidda gwani.
Jahar katsina ta tsaya matsayar cewa su indirect primary za suyi....wannan matsayar yanzu haka aka cim mata a taron masu ruwa da tsaki na jam iyyar da akayi a yau.

No comments:

Post a Comment