Thursday, 30 August 2018

PDP Ta Lashi Takobin Kayar Da Buhari Da Masari A Katsina A Zaben 2019 -Daga Jamilu Dabawa, Katsina




Babbar Jam'iyyar adawa ta PDP a Jihar Katsina ta Sha alwashi Kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamna Aminu Bello Masari a kakar zabe mai zuwa ta 2019.


Shugaban jam'iyyar PDP na Jihar katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron da jam'iyyar ta gudanar da masu son tsayawa takara 'yan majalisun jiha da kuma shugabanni jam'iyyar na kowane mataki, wanda ya gudana a helkwatar jam'iyyar da ke Katsina.

Majigiri ya kara da cewa "Ina da yakinin jam'iyyar mu ta PDP za ta samu nasarar lashe zabe mai zuwa a kowacce kujera har da ta shugaban Kasa duk da dan asalin jihar Katsina ne. Dalili kuwa shi ne babu wani abun azo a gani ko kuma wani aiki da jam'iyyar APC ta yi wa al'ummar jihar Katsina da za su fito su yi yakin neman zabe da shi, sai dai sun jefa al'ummar cikin halin fatara da talauci da kuma rashin aikin Yi ga matasa.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya cigaba da cewa duk mutumin da ke jihar katsina ya shaidi irin ayyukan alheri da jam'iyyar PDP ta shimfida a cikin shekarun goma Sha shidda da muka kwashe muna mulki da kuma gagarumin cigaba da jihar Katsina ta samu da kuma ayyukan da Gwamnatin tarayya ta yi a Jihar. Shi yasa al'ummar jihar suke da tabbacin idan ta dawo a 2019 za ta cigaba da ba yayansu ilmi kyauta da kuma gudanar da ayyukan da zai inganta rayuwar su.

Daga karshe ya yi ga yan takarkaru na jam'iyyar PDP da suke sayen form na kowacce kujera su zamanto ayi siyasa ta fahimta, babu batanci ga juna. A tafi a nemi jamaa duk Wanda Allah ya ba nasarar lashe zabe, wanda bai samu ba ya ba shi goyan baya domin ganin mun amshi kafatanin kujerun mu wato tun daga sama har kasa da yardar Allah a 2019.

No comments:

Post a Comment