Monday, 27 August 2018
Alaqar Jami’an Gwamnati Da Kirkirar Asusun Bogi ‘Fake Account’ A ‘Social Media’ Daga Saifullahi Mato
MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR KATSINA, SHUGABAN MAJALISAR DOKOKI TA JIHA, SHUGABAN JAM’IYAR APC NA JIHA, KWAMISHINAN YAN SANDA, JAMI’AN TSARON FARIN KAYA (SSS) DA MASU RUWA DA TSAKI.
Da yake wannan magana bata shafi siyasa kai tsaye ba, saidai gyaran lahira da zamantakewar rayuwarmu ni da ku.
Cikin girmamawa da biyayya irin ta 'Da da Uba (nida maigirma gwamna), tare da duba da halin da ake ciki, da kuma matsayina na halattaccen dan APC kuma masoyin Maigirma gwamna tun yana PDP a 2006 lokacin nine sakataren ‘Masari Campaign Organization’ na karamar hukumar kankara, sannan ina takarar kansila na kankara A & B zuwa yau.
Bisa ga kwakkwaran bincike tare da dinbin shedu mun gano alamun dake nuna wasu daga cikin manyan Jami'an gwamnatin katsina kuma na kusa da Maigirma Gwamna babanmu Rt. Hon. Aminu Bello Masari ne suke bude ‘fake account' a 'social media' don su rinka damfarar gwamna kudin aikin 'social media' da sunan zasu daqile batancin da ake, eh, saboda Idan ba su bane; me ya hana su bari a gayawa gwamna gaskiyar binciken da akai akan MALAM MATI KATSINA wanda an kama mutane sama da 10 har dani kaina ana sheri da canza bayanan tuhuma daga karshe a gayawa gwamna wani abun daban, ba abunda bincike ya nuna ba?
Da Wannan suke fakewa suna zuwa su fada wa maigirma Gwamna karya, suna kirkirawa mutane sharri, domin su yi masa ingiza mai kantu ruwa yana sanyawa ana kama mutanen da basu ji ba kuma basu kuma gani ba, bawan Allah duk baisan abunda ke wakana ba! Babu sheda kuma har yau sannan matsalar bata kare ba, sun kasa magancewa gwamna ita. (Muna da shedu)
Sannan muna da hanyar da za'a bi a magance matsalar, amma Wasu maqiya Allah, dake wa mutane sharri wajan gwamna sun hana mukai gareshi kuma sun hana Masana da kwararru akan harkar sukai ga ganin gwamnan don suyi mashi bayanin yadda abun yake adaina damfararshi kuma adaina daukar alhakin mutane da bata masu suna.
Muna kuma da hanyar da za'abi don jin 'Voice calls' ko bibiyar 'whatsapp chats' ko 'facebook inbox' da wadannan mutanan banzan keyi cikin dare suna munafunci, gulma da zagin gwamna gurin 'yan adawa amma da gari ya waye kuma sune gaba gaba wajan zuwa gaida gwamna da sunan masoya ko abokan aiki.
Haka kuma; akwai sheda ta hadin baki da ake da wakilan gwamnati da jami’an tsaro ba tare da sanin gwamna ba ana wulakantawa, azabtarwa da qago sharri da shedun karya ga ‘yan 'Social Media' na jihar katsina idan aka kama su, don a kaudawa gwamna hankali da sunan ana kama masu batanci da cin mutunci a 'social media' kamar yadda ake gaya mashi. (Wannan ma muna da shedu ba 1 ba, ba 2 ba)
Ataqaice dai In banda Allah na son maigirma gwamna da tun sadda wadannan mutanan suka fara wannan nukura da yanzu gwamnatinshi sun kore mata jama'a kaf musamman yan ‘Social Media’ saboda basu son wani na matsarshi inba su ba.
Bisa ga wadannan bayanai nike rokon gwamna da jami'an tsaro indai da gaske ake to su gayyaceni in bada sheda amma dole sai agaban maigirma gwamna, kuma a hada da yan jarida don kada a rufe maganar bayan asiri ya tonu na fadeta.
Daga yau kuma duk wanda ya kuskura ya kara alaqantani da 'facebook fake account' to wallahi kotu zata rabani dashi komin girmanshi.
Sannan ina kira ga masu ruwa da tsaki; kodai ku shiga cikin maganar nan ko ta haddasa fara daukar mataki da hannunmu, ko kuma duk wanda akai mawa ya rama akan wanda yayi mashi sharrin, ko ta jawo wani abun daban wanda ba'a san inda zai tsaya ba. Faqat.
Kuma Insha Allahu duk masu munafuntar Babanmu maigirma gwamna sai mun tona masu asiri 1 bayan 1 ko kuma su bari tunda wuri.
Allah ya taimaki jiharmu, gwamnan mu, jam'iyarmu da shugaban kasarmu.
Nagode
Saifullahi Mato
08162949976
E-mail:matokkr@gmail.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment