A yau Laraba ne kotun kula da ma’aikata, CCT, a Abuja ta kori karar da aka shigar gabanta wanda ake tuhumar Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da laifuka har 13, ciki har da yin karya wajen rage yawan kadarorin sa a lokacin da ya bayyana yawan dukiya da kadarorin da ya mallaka a lokacin ya na gwamnan jihar Kwara.
Jami’in gabatar da kara M.S Hassan ne ya rubuta tuhumomin da ake yi wa Saraki, inda aka yi ta tabka shari’a har tsawon shekaru biyu. Idan ba a manta ba, cikin watan Mayu, 2017, an kara yawan caje-cajen da ake tuhumar Saraki zuwa 17.
Tun cikin watan Satumba, 2017 ne aka fara maka Saraki kotu.
Wasu tuhume-tuhume da ake yi wa Saraki, sun hada da mallakar
dukiyar da ta zarce albashin sa da kuma bude asusun ajiyar kudade a kasashen
waje.
Tun lokacin da aka maka shi kotu, Saraki ya yi ta cewa ana yin
wannan shari’a ne don a bata masa suna ne.
Da yake karanta bayanin korar karar. Mai shari’a Umar, wanda tun
farko Saraki ya ce bai yarda ya yi masa shari’a ba, ya bayyana cewa mai gabatar
ga kara ya kasa gabatar da kwakkwaran hujjojin da za su tabbatar wa kotu cewa
Saraki ya aikata zargin da ake yi masa.
No comments:
Post a Comment