Kwamitin kula da ruwan sha na jihar Katsina ya kai ziyarar gane ma ido a garin Dutsinma.
Makasudin ziyarar
shine don ganewa matsalolin da irin hanyoyi da za a bi don magancewa da farfado
da Gidan ruwan dake Dutsinma. Kwamitin
ya samu shugabancin Abubakar Matazu wanda a inda yayi alkawarin mika sakamakon
bincikin su zuwa ga mai girma Gwamna Aminu Bello Masari.
Gidan ruwa na Dutsinma ya shekara 42 da budewa, kuma yanzu haka dakunan magani, da enginan genareta duka basayi.
Gidan ruwa na Dutsinma ya shekara 42 da budewa, kuma yanzu haka dakunan magani, da enginan genareta duka basayi.
Ana shi jawabin, shugaban
Gidan ruwa na Dutsinma Alh Yahaya ya mika godiya ga gwamnati Katsina ganin
yadda take ta kokari don raya wannan Gidan ruwa.
A satin da ya gabana,
Mai girma gwamna Masari ya fuskanci barazana a yayin daya kai wata ziyara na
rufe gasar wasan kwallo da akayi a garin Dutsinma. A inda mutanen garin
Dutsinma manya da yara suka fara mashi aho da jifa da duwatsu suna furta cewa “bamayi
bama su” ganin yadda gwamnatin tashi tayi watsi da matsalolin jama’ar Dutsinma.
Cin ko wannan turniki
ne ya jaza wannan ziyara na kwamitin ruwa ta kai ziyara zuwa Gidan ruwa na
Dutsinma?
No comments:
Post a Comment