Bisa la'akari da muhimmancin wannan kafar sadawa ta zamani da kuma rawar da take takawa a ciki da wajen wannan Jiha, Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari CFR ya amince da daga darajar wannan ofishi na kula da wannan kafa ta sadarwa.
Sakamakon haka, Mai taimaka wa Gwamnan (SA) ta wannan sashen, AbdulHadi Ahmad Bawa a yanzu ya zama Babban Mai taimaka wa Gwamnan (SSA), sannan kuma kowace shiyyar Sanata dake a wannan Jiha an nada mata Mataimaki na musamman kamar haka;
1. Aminu Darma - Shiyyar Katsina
2. Yulaks KY (Yusuf Lawal Kankia) - Shiyyar Daura
3. Mohammed Garba MG - Shiyyar Funtua
Muna yi wa Maigirma Gwamna godiya da fatar alkhairi bisa ga wannan karamci, muna kuma yi wa juna addu'ar Allah Ya bamu ikon sauke wannan nauyi yadda ya kamata.
No comments:
Post a Comment