Monday, 26 September 2016

IDAN BA KA CANJA BA TA K'AK'A ZA KA GA CANJI. !!!

BA KA CANJA BA TA K'AK'A ZA KA GA CANJI.!!!
Facebook -:|:- Ibrahim Garba Nayaya


Da yawa cikin mutane sun dauka canji shi ne a sauya shugaba; wanda hakan shi zai bayu zuwa ga gyaran al'umma, ko su fahimci canji shi ne kame wadanda suka aikata barna. Ko a tunaninsu wani mutum kadai shi zai kawo canji cikin al'umma. Hakan sai ya sanya fira a majalisu ba ta wuce ta zagin shugabanni ko la'antarsu, duk wai da sunan sun gagara wajen kawo sauyi, ko sun jefa mutane a bala'i, ko wai har yanzu ai ana kisa. Na'am, Mutane sun manta da abubuwa guda uku kamar haka:

1- Allah kadai kan samar da canji ba mutum ba, budi da qunci duk na gare shi shi kadai ba dan'adam bam, himma, dabara, qarfi, wayo ba su kawo canji, dukkan su sabubba ne, Allah kadai kan kawo canji.

2- Canji bai samuwa idan baka canja a niyar ka da halin ka ba, misali anan; kai dan kasuwa ne, me ka bari na daga cin riba ko ruwa? Kai ma'aikacin gwamnati ne, ta yiwu kai accounter ne, ko Head-master, ko malamin makaranta, ko shugaba a wani bangare, ko lebura a wata ma'aikata, ko yaro a gurin ubangidansa, ko me gida ne kai da yara a kasanka. To me ya canja cikin cuwa-cuwar aikinka ko wata almundahana?

3- Ba a samun canji ba tare da an gyara kofofin barna ba, wannan kuwa dole ya sa a ji jiki ko yaya yake, kafin abin ya mike.

Sanin kowane an zauna shekaru 16 cikin barna a wannan Kasa, kisa ya zama ruwan dare, cin hanci ya mamaye kowane ofis, karya da yaudara su ne tamburan da yawa daga cikin shugabanni, danne marar karfi da zalunci su ne kwalliyar shugabanni. Kowane shashasha sai ya zo ya yi abinda ya ga dama, ko da sunan shugabanci ko addini ko wakilci. To shin ta ya ya dare guda za a wayi gari a ga an samu sauyi.

Shin kun manta gwamnatin da ta shude, ana kashe ba sa jajanta muku, bal ma a daidai lokacin suna can suna rawa akan minbarin siyasa, kun manta suna kallo ana kace shanunku duk da haka cikinsu babu wani mai hankalin da yake tausaya muku. Shin kun manta halin da 'yan'uwanku a jihohin Adamawa, Borno da Yobe suka samu kansu, na firgici da tashe-tashen hankula, ba ka da damar fitowa sallar da ta zama dole ga dukkanin musulmi! Kasuwanni da tashoshin mota duk sun zama matattara ta kashe al'umma, mutane na gudu a cikin dazuka domin tsira da rayukansu, ba sa tunanin ruwa ko guziri ko abinci, ko katafaren gidan da ya mallaka ko dukiyar da ya taskance. Ganyen maina shi ne mafi kyawun abincinsu, kafafuwansu ba takalma tare da tsananin zafin rana kamar yadda tsananin sanyin hunturu ba ya sanya su koma gidaddajinsu.

Tashin bama-bamai, da garkuwa da mutane ko kashe wane da wane, su ne mafi labaran da muke karya kumullo da su, har ma idan aka wayi gari ba a ji dayan cikin ukun labaran nan ba, to za a rinka taya juna murna ce. Tsanani ya kai tsananin da uwa ta tserewa 'ya'yanta, kamar yadda uba ya gudu ya bar iyalansa, tare da tsananin so dake rataye a zukatan wadannan bangarori. Kisa ba babba ba yaro, ba mace ba namiji, ba dattijo ba jariri, sarakuna da malamai da yan siyasa da yan kasuwa da talakan da ya fito leburanci.

Wajibi ne kowa ya gyara kura-kurensa, ya gyara mu'amalarsa, ya nesanci barnar da yake yi, sannan ya yi wa shugabanninsa addu'a. Ahmad Bn Hambal yake cewa "Da ina da wata addu'ar da na san karbabbiya a gun Allah, da shugabana zan yi wa". Imam Barbahari yake cewa "An umarce mu da mu yi musu addu'ar gyaruwa, ba a umarce mu da mu yi musu addu'ar halaka matukar suna nan a matsayinsu na shugabanninmu koda sun yi zalunci sun ketare iyaka.............. idan ka ga mutum yana yiwa shugaba addu'ar halaka, to ma'abocin son zuciya ne. Idan ka ga yana musu addu'ar shiriya to ma'abocin sunna ne insha Allah".

Kowa ya sani "LALLE ALLAH BA YA CANJA ABINDA KE GA MUTANE HAR SAI SUN CANJA ABINDA KE ZUCIYOYINSU".Ibrahim Garba Nayaya07066366586.

No comments:

Post a Comment