Wednesday, 20 July 2016

Babban Sako Zuwa Ga Sashen Ilimi Na Jihar Katsina. Daga Sani Hamza Funtua

Ofishin: Gwamnan Jihar Katsina. S.A & P.A akan harkokin Ilimi.
 Kwamishinan Ilimi na Manyan Makarantu.
Vice Chancellor na Jami’ar Ummaru Musa Yar’adua.
UMARU MUSA YAR’ADUA UNIVERSITY KATSINA
©Sani Hamza Funtua™

Ilimi a Jihar Katsina shine arziki na biyu da Jihar ta daga bayan arzikin Noma, har za’a iya samun a wasu shekarun farashin Noma kan fadi a kasuwa amma Farashin Ilimi na nan yadda yake saima kara hau-hawa da yake yi. Duka wannan na daga cikin ni’imomin da Allah ya saukarwa wannan Jiha ta Katsina mai albarka. Tsawon shekarun da makarantun gaba da Sakandire a wannan Jiha sukayi, kama tun daga [Univiersity, Federal Politechnic, State Politechnic, Colleges d.s], har zuwa yanzu ban taba jin ance yau ga shekarar da makaranta daya daga cikin su ta yaye dalibai Marasa Ilimi ba.

Jahar Katsina ta shahara ainun wajen yaye dalibai hazikai kuma nagartattu a Kasarmu Nigeria. Duba da tsohuwar makarantar horar da Malamai wato [KTC] ko ince [ATC], inda shuwagabanni da yawa sunyi ilimi a ciki kamar su Abubakar Tafawa Balewa, Sardauna of Sokoto da Sauran su. Bari inje kai tsaye yanzu ga Makalar dana dauka a sama, wannan Jami’a ta Ummaru Musa ta shahara a idon Duniya, dalibai daga kasashe da dama na zuwa don samun ilimi, hakan yasa ake sa ran Makarantar zata shiga sahun Goman Farko a jerin Jami’o’in kasar nan masu kokari a shekaru masu zuwa. Sai dai Kash.! Iya tunani na da tunanin mutane da dama, jami’ar ta rasa wasu manya-manyan sashuna na koyarwa wadan da a wannan zamanin fannonin ne ke karbuwa da samun daraja a Duniya. Da farko dai a Jami’ar babu Fannin kere-kere [Engineering].


Wannan ba karamin rami bane da makarantar ke da shi, wanda ka iya zama kamar nakasu a idanun jama’ar wannan kasa dama duniya baki daya. Sanin kowa ne [Engineering] fanni ne da a yanzu ke cin Karen shi ba babbaka a duniyar daukar aiki, sannan ko mutum bai samu aikin gwamnati ba, zai iya yin aiki don kashin kansa kuma yaci nasara ta rayuwa. Sai gashi a wannan Jami’ar an kasa samar da wannan Fanni na [Engineering]. Fanni na Biyu kuwa wand azan iya cewa ya kusa fin na farko shine fannin Tsare-tsare na Gari da kasa [Eniviromental Technology]. A cikin wannan Fannin, akwai sashe-sashe kamar su, [Architecture, Building Tech, Quantity Survey, Survey & Geo Impor, Design, Estate Management, Town Planning, da sauran su.].

A zahirance zamu ga cewa, wannan fannin shine a yanzu diniya tafi maida hankali kanshi duba da yadda Al’umma suka dukufa wajen yin manya-manyan Gine-gine. Idan na tsaya akan wadan nan biyun kadai, zan iya cewa, ba karamin Nakasu Jami’ar ta Umaru ta samu ban a rashin wadan nan Fannoni na Ilimi. Na tabbata idan da za’a samar dasu da Jahar Katsina ta fi ko wace Jaha shahara a fannin Ilimin jami’a bayan Ahmadu Bello da jami’ar Bayaro. Duk da cewa jami’ar Usumanu Danfodiyo dake garin Sokoto ta zarce jami’ar ta Umaru a yanzu, shigo da sababbin kwasa-kwasan zai sanya jami’ar ta Umaru ta kere ta Usumanu Danfodiyo dama sauran tsararrakinta. Da wannan nike kira ga Gwamnatin Jahar Katsina karkashin mahukanta a bangaren Ilimi dasu duba wannan bayani nawa, sannan su duba daraja da martabar da Ilimi ke da shi a wannan jaha tamu, su samar da Wadannan fannoni na [ School of Enigineering da School of Enviromental Technology].

Hakika samar dasu zai kara habbaka ilimi a wannan jaha, sannan zai rage yawan fitar ‘yan asalin jahar zuwa wasu jahohi don yin karatu a wadan nan Fannoni, haka zalika za’a samar da jajurtattun dalibai da nan gaba kasarmu zatayi alfahari dasu kamar yadda tarihi ya nuna a baya kuma muke fatan ya mai-maita kanshi. 
#AllahRayaJaharKatsina.

Daga:- Sani Hamza Funtua.

 07032183026

Sanihamza123@Naij.com

No comments:

Post a Comment