Makarantar
College na koyan ilimin Karatu watau “Isa Kaita College Of Education” dake
Dutsinman, Katsina ta amince hadin guiwa (MOU) da jami’ar Ahmadu Bello
University Zaria wajen tsarin tafiyar da salon karatu na degree da Isa Kaita College
zata fara.
A na shi
bayanin, shugan Makarantar “Isa Kaita college of Education” Maigari Audu ya
nuna jin dadin sa bisa yadda Jami’ar A.B.U Zaria ta amince don kaddamar da sashen
bada ilimi na Degree a Isa Kaita amma a karkashin kulawar ita jami’ar A.B.U
dake Zaria.
Wakilin “Vice
Chancellor” na jami’ar Ahmadu Bello University zaria Ibrahim Sule ya baiyana
sun yi amfani da sakamakon bincike da “NUC” da kuma binciken da masana ilimi suka
gudanar akan cancantar “Isa Kaita
College Of Education” wajen fara bada ilimi da certificate na Degree.
Ya kuma kara
da cewa jami’ar A.B.U Zaria ta kammala shirye shirye domin fara bada horu ga Mallaman
“Isa Kaita College Of Education” domin zai inganta kimar ilimin da dalibai zasu
samu.
Daga Karshe
Kungiyar “NUC” ta amince da “Isa Kaita College of Education” da ta fara da
darrusa (courses) kamar haka;
BSC Ed (chemistry,
physics, biology, computer science, agricultural science, Islamic studies da
kuma hausa language).
GASKIYA WANNAN YAYI ALLAH YABADA SAA
ReplyDeleteAllah sa albarka acikin wannan cigaba da yazo mana.
ReplyDeleteAllah ya taimaka ya kuma kara tsare mani Dr. Abdu Maigari Saboda kokarin da yake na kawo ci gaba a wanann makaranta
ReplyDelete