
Charles Okah kani ne ga Henry Okah, Ga yadda
jaridar Sahara Reporters ta baiyana cewa “ Wakilinta ya samu labarin da ga
wani ma’aikacin Gidan yarin ne. a inda yace masa Charles Okah ya daga tsalle
misalin karfe 7:30pm ta Katanga Gidan yarin da ke nan Kuje, Abuja".
Kafin ya aikata wannan ta’asa, ma’aikatan Gidan yarin
sun ganshi ne tare da wani abokin zaman shi a nan cikin Gidan yarin, wanda daga
nan ba a sa ke ganin shi ba.
Abun tambaya a nan shine? Duk tsayon girman
katangar gidan yari ta ya ya zai samu abin da zai taka ya daka tsalle domin
hawar wannan Katanga?
Koko a wajen katangar babu masu tsoron gadi ko da ta baci irin haka wadda ta
faru? Shin koko dai ma hadda hadin masu tsaron wurin?
To, wannan dai idan ta yi tsami za mu ji duk yadda
abun ya kaya. Amma dai tuni 'yan sanda da sauran jami’an tsaro su dukufa wajen
binciken gano shi watau Charles Okah.
No comments:
Post a Comment