Friday, 24 June 2016

An Gudanar Da Zanga-Zanga Akan Yadda Mustapha Inuwa Yayi Babakere a Harkar Matasa a Katsina

Matasan jam’iyar  APC rashen jihar Katsina tare da hadin kan dalibai sun gudanar da wata babbar zanga-zanga a gaban Gidan gwamnatin jihar Katsina don nuna batan ci da tauye masu hakki da Magatakardan Gwamnatin Katsina Dr Mustapha Inuwa ya yi kuma ya ke cikin yi a yanzu haka.
Taron zanga-zangan ya hada da tsofaffin mata da matasa daban daban daga kowane sashe a cikin jihar Katsina wanda su na ta korafi akan irin yadda Dr Mustapha Inuwa yayi baba-kere da handama da kuma butulce ma irin alkawarin tallafa masu da gwamnatin RT. Hon Aminu Bello Masari ta dauki alkawarin niyar taimaka masu.
Wakilin Cliqqmagazinehausa.blogspot.com ya fahimci cewa matasan da taron jama’a da suka hallarci wannan zanga-zanga sun bauta ma wannan gwamnati wajen yakin ta na ne man cin zabe da ya gudana na shekarar 2015, Wanda suka yi yar jejeniya ta cewa gwamnati zata tallafa masu da hanyoyi da za su fara sana’oi iri daban daban.
To amma yanzu shekara daya kenan babu alamar cika masu wannan alkawari da gwamnati tayi. Wasu kuma daga cikin su sun ce Sakataren gwamnati Dr Mustapha Inuwa ya shigo yayi baba-kere a maganar wanda har ma yana yin korafi da cewa “su mutanen banza ne, Yan iska marasa abun yi, kai ma har Gidan yari [prison] zai sa a kai su idan basu maida hankali ba ga cewar su amma a wani video da ke yawo a yanar gizo-gizo na sadawar Facebook”.

Da yawansu sun dan gana halaiyar Mustapha Inuwa da abun kyama da zalunci wanda yasa ma irin hakan tasa marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ya kure shi daga Sakataren gwamnati a lokacin ya na gwamnan jihar Katsina.
Daga bisani ma wasu sun yi aman na da cewa ishara ce Allah ya ke nuna ma mutanen Katsina akan irin butulci da suka yi ma Gwamna Shema wanda gashi tun ba aje ko ina ba gwamnatin APC da irin su Dr Mustapha Inuwa Sun Fara butulce wa jama’ar da su ka sha wahala wajen zaben su.
To, Ko ya zata kaya? Gwamna Masari ne kawai zai iya bada tabba tattaciyar amsa akan ko…. gwamnatin shi zata cigaba da Mustapha Inuwa koko zai yi bincike iya binciki akan yadda mutanen katsina ke kalubalantar halaiyar Mustapha Inuwa wajen kamanta adalci da gaskiya.

No comments:

Post a Comment